An yi atisayen ƙarshe na dukkan fannoni don share fagen karɓar Kumbon Shenzhou-14

Daga CMG HAUSA

Da daren jiya Alhamis 1 ga wata ne aka gudanar da atisayen karshe daga dukkan fannoni, don share-fagen karbar kumbon Shenzhou-14. Kawo yanzu, an shirya tsaf don maraba da dawowar kumbon duniyar mu.

Bisa shirin da aka tsara, bayan da ‘yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-14, suka mika ayyukansu ga takwarorin su dake cikin kumbon Shenzhou-15, za su dawo doron duniyar nan ba da jimawa ba.

Mai fassara: Murtala Zhang