An yi hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet), ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.

Hukumar ta ce, jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntar jihohin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.

Tuni dai dama ambaliyar ta fara ɓarna a wasu jihohin Nijeriya inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

“A yankin Arewa ta tsakiya, ana hasashen samun ambaliyar ruwan a sassan Neja, Nasarawa, Benuwai, Kwara, Babban Birnin Tarayya da Jihohin Filato da safe.

“A washegari, ana sa ran za a yi tsawa da ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Filato, Nasarawa da Kogi.

NiMet ta ce, “A cikin sa’o’in safiya, ana sa ran hadari zai sararin samaniyar yankin kudu.”

Hukumar ta yi tsammanin samun ruwan sama na kamar da bakin kwarya a wasu sassan jihohin Osun, Oyo, Ekiti, Ebonyi, Enugu, Anambra, Cross Riɓer, Ribas, Delta, Bayelsa da Akwa Ibom.

NiMet ta ce, ana hasashen tsawa a wasu sassan jihar Taraba da safiyar ranar Talata.

“Da rana zuwa yamma, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Bauchi, Kaduna, Kebbi, Gombe da Yobe.

“A yankin Arewa ta tsakiya, ana sa ran samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu sassan Jihohin Filato da Nasarawa da safe.

“Da rana da yamma, ana sa ran za a yi tsawa da ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Nasarawa, Benue da Filato,” inji shi.

Hukumar NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama a wasu sassan Jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom da ke da ƙarancin ruwa a wasu sassan yankin kudancin ƙasar da safe.

By ukarofi