An yi kira ga shugaban NLC na ƙasa ya bada tasa gudunmawar wajen samar da tsaro a Arewacin Nijeriya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamred Mannir Suleiman tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikatan kiwon lafiya na ƙasa reshen Jihar Katsina a wata hira da manema labarai a Katsina ya bayyana.

Ya ce wajibi ne shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa Mr Joe Ajero ya bi ta ƙungiyar sa wajen lalubo hanyoyi da za a bi a dawo da zaman lafiya a Arewacin ƙasar.

“Ina kira ga ƙungiyoyin ƙwadago,addinai, siyasa da manyan Arewa su haɗu cikin gaggawa domin lalubo hanyoyi da za a bi a magance ta’addanci tun kafin durƙushewar Arewacin ƙasan,”Inji kwamred Suleiman.

Kwamred Mannir Suleiman wanda harwala yau shine shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua ya ce babu inda ke da tsaro a jihohin Arewa,domin haka a cewar sa dole ne a lalubo hanyoyi da za bi don dawo da zaman lafiya.

Ya ce duk da gwamnatocin tarayya, jiha da kuma ƙananan hukumomin bisa ƙoƙarin da suke wajen magance ta’addanci, Yakamata su ƙara ƙaimi wajan tunkarar matsalar domin a kullum kashe mutane ake yi da lalata dukiyar su.

Kwamred Suleiman ya kuma shawarci shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa da ya haɗa kai da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro domin fito da wasu tsare-tsare da dabaru na yadda zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci a jihar.

Ya yabawa wa Mr Joe Ajero bisa yadda yake jagorancin ƙungiyar da jajircewa wajen abinda ya shafi haƙƙokin ma’aikatan a kasar.

By ukarofi