Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
‘Yan sanda a ƙaramar hukumar Haɗeja sun sami labarin yankan rago da wasu mutane da ba a san ko su waye ba su ka yiwa wata amarya wadda ba ta wuce sati biyar da angwance wa ba. Lamarin ya faru a cikin gidanta da ke unguwar Warware a garin Haɗeja .
Kamar yadda bayanan ƴan sanda ya nuna , sun Sami labarin kisan da aka yi wa matar ne bayan da maƙotan gidan suka sanar da su ,matar mai suna Zainab Ibrahim ýar shekara 22 da haihuwa sun same ta male male cikin jini a kwance bata motsi, amma duk da haka suka garzaya da gawarta babban asibitin Haɗeja, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da mutuwar ta.
Kakakin rundunar ƴan sanda na Jihar Jigawa SP Lawan shisu Adam ya tabbatar da faruwar labarin, ya kuma ƙara da cewar yanzu haka ƴan sanda sun duƙufa da gabatar da bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su a gaban kuliya domin girbar abinda suka aikata.
