
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Litinin ne ƙasar Chana ta buɗe ƙofar ƙarfafa alaƙa tsakaninta da shugabannin ƙasashen Afirka don bunƙasa ayyukan ci gaba a Nahiyar Afirka a wani taron da aka yi wa laƙabi da Chan-Africa.
A makon nan ne ƙasar wani rahoton gidan jarida na ƙasar Beijing ya ce taron haɗin-gwiwa na China-Africa zai zama babban fagen harkokin difulomasiyya tun lokacin annobar COVID-19 wanda ake tsammanin wakilci da dama daga ƙasashe daban-daban.
Ƙasar Chana ta aika da dubunan ma’aikata zuwa Afirka don gina manyan ayyukanta musamman a ɓangaren albarkatun ƙasashen.
Yawaitar adadin kuɗaɗen aro da Chana ka bai ƙasashen Afirka sun taimaka wajen haɓaka ababen more rayuwa, amma kuma a gefe guda sun bar ƙasashen da tarin bashi.
A halin yanzu dai ƙasar Chana ita ce babbar abokiyar hulɗar kasuwanci da Nahiyar inda alaƙar da aka ƙarfafa ake fatan za ta samar da gobe mai kyau musamman ga Nahiyar ta Afirka.
Cikin ƙasashen da suka samu wakilci a taron akwai Nijeriya da Afirka ta Kudu da Jamhuriyyar Congo da sauran su.
