Yau za a fara shari’ar masu zanga-zanga a wasu manyan jihohin Arewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yau ne ake fara shari’ar masu zanga-zanga a jihohin Abuja, Kano, Kaduna da Borno, inji Mataimakin Sufeton ƴan sanda (DIG) ɓangaren Leƙen Asiri, Dasuƙi Galadanchi.

Mataimakin Sufeton ya faɗi haka ne a yayin taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) inda ya ce mutane 126 da aka kama za a gurfanar da su gaban kotu waɗanda ake zargin su da ɗaga tutar ƙasar Rasha da ke nuna buƙatar sauya Gwamanti a lokacin zanga-zangar wacce ta canja salo zuwa tashin-tashina da mace-macce gami da satar dukiyoyin ƙasa da ta al’umma.

Lauyan kare ƴancin Ɗan-adam Femi Falana tare da wasu lauyoyi za su tsaya gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja don kare ƴan zanga-zangar.

An kama waɗanda ake zargin ne yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta sakamakon tsarin cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi tare da rugujewar darajar Naira waɗanda suka sabbaba matsin rayuwa da al’ummar Nijeriya suka tsinci kansu a ciki.

By Babaji