Yadda ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona a Neja da Kebbi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona a ƙaramar Hukumar Argungu da sauran yankunan da abin ya shafa a jihohin Kebbi da Neja.

Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Hukumar Raya Wutar Lantarki ta ƙasa (N-HYPPADEC), Nura Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, yayin da yake jajantawa manoman da iftila’in ya shafa.

Hukumar ta ce tana kallon lamarin a matsayin wani gagarumin koma baya ga ƙoƙarin da al’ummar ƙasar ke yi na samar da ɗorewa da tabbatar da abinci.

Sanarwar ta ce, Manajan Daraktan Hukumar, Abubakar Yelwa, ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda ambaliyar ruwan ta shafi rayuwar al’ummar da dama.

Ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya bisa matakin gaggawar da ta ɗauka na ware Naira Biliyan 3 domin tallafawa waɗanda bala’in ya rutsa da su.

A baya dai hukumar ta gudanar da gangamin wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai da ziyarce-ziyarce, wanda hakan ya taimaka wajen rage illar da ambaliyar ruwa ke yi wa al’ummar da ke kisa da teku.

Hakazalika, ambiyar ta tafi da gonakin da ke kusa da wuraren ruwa.

N-HYPPADEC ta jaddada buƙatar gaggawa na kiyaye ƙa’idojin aminci daga al’ummomin da abin ya shafa.

Wannan lamarin dai na zuwa ne bayan hasashen da hukumar kula da ruwa ta Nijeriya NIHSA ta yi na nuna ƙaruwar ruwa a kogunan Rima da Nijar, sakamakon rahoton da hukumar kula da yankin Neja ta NBA a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ta samu.

NIHSA ta yi gargaɗi game da ƙarin ambaliyar ruwa saboda ayyukan da ake yi a Nijar da Mali. Ana sa ran waɗannan ambaliyar ruwa za su shiga Nijeriya sannu a hankali, wanda ke zama babbar barazana a cikin kwanaki masu zuwa.

Aƙalla mutum 49 ne suka mutu, sannan dubbai suka rabu da muhallansu bayan mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya a Arewacin Nijeriya, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya ta sanar a ranar Litinin.

Jihohin Arewa guda uku da suka fi fuskantar ambaliyar su ne Jigawa da Adamawa da Taraba, kamar yadda Kakakin NEMA Manzo Ezekiel ya shaida.

A shekarar 2022 ce Nijeriya ta yi fama da ambaliya mafi muni a cikin shekakarar da suka gabata, inda mutum 600 suka mutu, sannan kusan mutum miliyan 1.4 suka rasa muhallansu, sannan aaalla hekta 600 na gona ya lalace.

“Yanzu ne muke shiga ƙololuwar damina, musamman a Arewacin ƙasar,” inji Ezekiel a tattaunawarsa da Reuters.

Haka kuma ambaliyar ta lalata kusan hekta 694 na gonaki.

Idan ba a manta ba, tun a farkon daminar bana Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa jihohi 31 daga cikin 36 ne suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa.

By ukarofi