Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙungiyar Masu Sarrafa Kwakwar Manja ta Nijeriya (NPPAN), Ambasada Alphonsus Inyang, ya samu nasarar zama shugaban ƙungiyar Masu ƙananan Gonakin Kwakwar Manja ta Duniya (WCOPS), bayan an zaɓe shi ba tare da hamayya ba a Gabashin Kalimantan, da ke ƙasar Indonesia.
An bayyana zaɓen nasa a matsayin babban ci gaba ga masana’antar noman kwakwar manja ta Nijeriya.
Majalisar WCOPS ita ce mafi girman sashen yanke shawara a cikin aungiyar, wadda aka kafa ƙarƙashin jagorancin Majalisar ƙasashen da ke Samar da Manja (CPOPC), tare da goyon bayan gwamnatocin Indonesia da Malaysia, ƙungiyar SOLIDARIDAD, ƙungiyar Samar da Manja Mai ɗorewa (RSPO) da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar a duniya.
ƙungiyar ta mayar da hankali ne wajen bunƙasa noman manja da inganta rayuwar manoma masu ƙananan gonaki a faɗin duniya, tare da kare haƙƙoƙinsu da muradunsu.
Ambasada Inyang, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban WCOPS mai kula da Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya samu sabon muƙamin ne tare da wasu shugabannin da aka zaɓa a taron.
Daga cikinsu akwai Dakta Gulat Manurung daga Indonesia, wanda ya zama shugaban ƙungiyar; Dakta Napoleon Ningkos daga Malaysia, mataimakin shugaban da ke kula da Asiya da Turai; da Tuan Haji Azimi Bin Hassan, shi ma daga Malaysia, wanda aka ba alhakin kula da yankin Asiya, Pacific da Oceania.
Sauran sun haɗa da Mista Allan daga Honduras, mataimakin shugaban da zai kula da nahiyar Amurka, da Dakta Djono Albar Burhan daga Indonesia, wanda aka naɗa babban daraktan gudanarwa. Haka kuma, an naɗa Dakta Paul Amaning daga Ghana a matsayin daraktan bunƙasa fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire.
An gudanar da babban taron zaɓen ne a sabon babban birnin Indonesia da ke Gabashin Kalimantan, yayin taron ƙasa da ƙasa na manoman manja masu ƙananan gonaki.
Taron ya samu halartar wakilai sama da 400 daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da manyan jami’ai daga Majalisar ƙasashen da ke Samar da Manja (CPOPC), ƙungiyar Samar da Manja Mai Dorewa (RSPO), SOLIDARIDAD, ƙungiyar Manja ta Indonesia (IPOA), Hukumar Kula da Manja ta Malaysia (MPOB), Majalisar Manja ta Malaysia (MPOC), da Hukumar Gudanar da Asusun Bunƙasa Gonakin Manja ta Indonesia (BPDP). Haka kuma, wakilan gwamnatocin Indonesia da Malaysia sun halarci taron.
A yayin taron, mahalarta sun amince baki ɗaya da buƙatar haɗa kai wajen kare haƙƙoƙi da muradun manoma masu ƙananan gonakin manja sama da miliyan 50 a faɗin duniya.
Ambasada Inyang ya daɗe yana fafutukar kare haƙƙoƙi da muradun manoman manja masu ƙananan gonaki. Haka kuma, shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwararru ta fasaha da ke kula da dabarun bunƙasa noman manja a Nijeriya daga shekarar 2026 zuwa 2050.
Baya ga haka, shi ne wakilin CPOPC a Nijeriya, ƙwararren mai ba da shawara kan harkokin manja a ƙasashen duniya, kuma shugaban ƙungiyar da ke nazarin hanyoyin inganta amfani da ragowar manja wajen samar da makamashi da sauran kayayyaki.
Ya kuma halarci tarukan ƙasa da ƙasa da dama da suka shafi noman manja, inda ya yi alƙawarin wakiltar Afirka yadda ya kamata a sabon muƙamin da ya samu a ƙungiyar.
