Ana ci gaba da biyan ‘yan hidimar ƙasa N33,000 duk da sabon tsarin albashi na N70,000

Spread the love

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta biya masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) alawus ɗinsu na watan Fabrairu da har yanzu yake kan tsohon adadin ₦33,000, duk da cewa an riga an sanar da ƙarin albashi zuwa ₦77,000. Wannan lamarin ya zo ne bayan alƙawarin da aka yi tun daga watan Janairu cewa za a fara biyan sabon adadin daga watan Fabrairu.

Wasu matasa da ke bautar ƙasa sun tabbatar da karɓar alawus ɗinsu a ranar Juma’a da daddare, amma sai suka ga cewa ba a aiwatar da ƙarin da aka alƙawarta ba.

A cewar Daraktan Janar na NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ƙarin alawus ɗin ya riga ya sami amincewa daga gwamnati, kuma abin da kawai ake jira shine amincewar kasafin kuɗi.

Matakin jinkirin biyan sabon alawus ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin matasan da ke yi wa ƙasa hidima. Wani mai bautar ƙasa daga jihar Oyo ya nuna damuwarsa, yana cewa “Gwamnati na son mu rayu da ₦33,000 a halin matsin tattalin arzikin da muke ciki? Sun ce za mu fara karɓar ₦77,000 a watan Fabrairu, amma yanzu sun ƙi cika alkawari.”

A Kano, wata baiwar Allah da ke hidimar ƙasa ta ce wannan lamari yana nuna yadda gwamnati ke nuna rashin kula da halin da matasa ke ciki. Ta ce, “Muna hidima wa ƙasa amma ba ma iya samun abinci mai kyau. Sun san ₦33,000 bai isa ba, amma sun ƙi cika alƙawarin su.”

Har yanzu dai gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa kan dalilin rashin aiwatar da sabon adadin albashin ba, lamarin da ke barin matasa cikin damuwa da rashin tabbas kan makomar sabon alawus ɗin da aka alƙawarta.

By ukarofi