IBB ne ya shirya yadda Abacha zai karɓe mulki kafin zaɓen June 12, inji Janar Ishola

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani babban soja a zamanin mulkin soji a Nijeriya mai suna Janar Ishola Williams (mai ritaya), ya musanta ikirarin da Tsohon Shugaban mulki soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya yi a littafinsa da aka fitar a kwanan nan.

Ya ce, IBB ne ya kimtsa yadda marigayi tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha zai karɓe mulkin tun kafin zaɓen rana 12 ga watan Yuni, 1993 da aka soke.

Janar Williams na ɗaya daga cikin waɗanda IBB ya lissafo a littafinsa mai shafuka 420 mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka ƙaddamar a ranar 20 ga watan Fabrairu a Abuja.

A cikin littafin ne kuma a karo na farko, IBB ya tabbatar da cewa MKO Abiola shi ne wanda ya lashe zaɓen ‘June 12’.

A lokacin da ya ke magana game da zaɓen a shafi na 296, IBB ya tabbatar da cewa zaɓen shi ne mafi sahihin zaɓe da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya.

Saida, duk da waɗannan kalaman na IBB, janar Ishola ya ce shi ne wnada ya tsara yadda Abacha zai gaje shi a mulki tun kafin a soke zaɓen.

Ya ce, ya halarci taron da aka kira na janar ɗin sojoji wanda a ciki akwai IBB da Abacha, inda a nan ne aka ƙaddamar da shirin.

Ya kuma ce, IBB ya manta da lokacin da ya ke kiran Abacha da ‘Khalifa’, wanda hakan ishara ce ta cewa shi zai gaje shi bayan ya sauka daga karagar mulki.

Haka kuma, Ishola ya ce ya taɓa rutsa IBB a gidan masukin baƙi na Shugaban ƙasa dake Minna a Jihar Neja, inda ya buƙaci IBB da ya tabbatar masa da cewa ya yi rantsuwa akan cewa Abacha ne zai gaje shi, amma ya ƙi ba shi amsa.

By Babaji