Shettima ya wakilci Tinubu a ta’aziyyar Shugaban Namibiya na farko, Nujoma

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa marigayi Shugaban Ƙasa na farko na Namibia, Dr. Sam Shafiishuna Nujoma, yana mai bayyana shi a matsayin jarumi da ya tara goyon bayan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka don ‘yantar da ƙasarsa.

A ranar Asabar ne aka gudanar da jana’izar ƙasa ta marigayi Nujoma a Heroes’ Acre, Windhoek, Namibia, inda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Tinubu a wurin bikin tare da shugabannin gwamnatoci daga sassa daban-daban na Afirka.

Shettima ya bayyana cewa rasuwar Nujoma ba wai ficewarsa daga duniya ba ce, illa kuwa matsayinsa na gwarzo da zai ci gaba da rayuwa a zukatan ‘yan Afirka.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa Nujoma ba kawai jarumi na ƙasarsa ba ne, amma wani jigo da ya yaƙi danniya da zalunci, tare da jagorantar Namibia daga mulkin mallaka zuwa zaman ‘yanci.

Ya kuma gode wa marigayi bisa gina ƙasar bayan samun ‘yancin kai, yana mai cewa Nujoma ya sadaukar da jin daɗinsa domin ‘yancin al’ummar Namibia. Bugu da ƙari, shugaba Tinubu ya tunatar da irin gudunmawar da Najeriya ta bayar a gwagwarmayar ‘yantar da Namibia, yana mai cewa dangantakar ƙasashen biyu ba za ta taɓa yankewa ba.

By ukarofi