Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Gwamna Nasir Idris ya ƙaddamar da kwamitin tuntuɓa da sulhu na masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC da nufin sanyaya zukatan waɗanda ake ganin ba’ayi masu daidai ba, musamman a yanzu da ake fuskantar zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.
A lokacin wannan bikin a Birnin Kebbi, Kwamred Idris wanda mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida ya wakilta, ya bada tabbacin cewar har yanzu APC a jihar Kebbi gidan aminci ne, tsintsiya maɗaurinki ɗaya, kuma ‘ya’yan jam’iyyar manufarsu guda, amma duk da haka, akwai buƙatar ko kana da kyau ka kara da wanka.
Ya ce yin haka akwai fa’ida domin an gudanar da zaɓen fidda ‘yan takara na matsayin siyasa daban daban, wanda watakila wasu bai masu daɗi ba.
Gwamnan ya yi bayanin cewar APC na son ta tattaro duk magoya bayan jam’iyyar zuwa muhalli ɗaya jajirtacce.
Ya ce maƙasudin kwamitin shine ya sanyaya zukatan waɗanda suka yi fushi ko suke da ƙorafe ƙorafe, domin ayi tafiya tare da nufin samun nasarar zaɓen da za’ayi mai zuwa.
Kwamred Idris ya ce gwamnati na buƙatar kowa da kowa ya ɓata goyon baya da haɗinbkai da biyayya wurin raya jihar Kebbi, abin alfaharinsu.
Shi kuma shugaban Kwamitin, Manjo-Janar Muhammadu Magoro, murabus, Galadiman Zuru, ya ce wakilan kwamitin za su ziyarci dukan ƙananan hukumomin 21 da ke jihar cikin kwanaki goma sha ɗaya na wa’adin kwamitin.
Janar Magoro ya ce zasu tattauna da shugabannin APC na ƙananan hukumomi (Exco members), da masu ruwa-da-tsaki da shugabannin mata da kuma ƙungiyoyin matasa.
Ya ce za su kuma gana da ma’aikatan gwamnati ƙarƙashin shugaban ma’aikata da kuma shugabannin manyan makarantu da suka ƙunshi mataimakan shugabannin jami’oi (Vice Chancellors) da kuma shugabannin kwalejojin kimiyya da kuma na Ilmi (Rectors, Provosts), da kuma Kwamishinoni waɗanda sune wakilan majalisar zartarwa ta gwamnati.
Haka kuma, ya ce zasu tattauna da uwayen ƙasa da kuma hakimai, sannan kuma su kai ziyarar ban girma ga fadar mai martaba Sarkin Gwandu wanda shine shugaban majalisar sarakuna ta Jihar Kebbi, domin sauraren shawarwari daga manya masu martaba sarakuna huɗu da ake da su a jihar, Masarautar Gwandu da Kabin-Argungu da Yauri da Zuru.
Janar Magoro ya ce wajibine duk ‘yan takaran da aka tsayar na majalisar dattijai da majalisar wakilai ta tarayya da kuma majalisar dokoki ta Jiha, su zo ayi wannan zagayawa ta tattaunawa tare da su saboda muhimmancin aikin.
Sauran waɗanda suka yi jawabi sune shugaban kwamitin na zama-tare (Co-Chairman) tsohon babban alƙalin Jihar Kebbi, (Chief Judge), Justice Muhammad Suleiman Ambursa, da kuma jami’in gudanarwa na kwamitin (Coordinator), kwamishinan ayyuka na Jihar, Hon. Engr. Abdullahi Umar Faruq Muslim.
