APC reshen Bayelsa ta dakatar da Lokpobiri da wasu jiga-jigan jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI

Jam’iyyar APC reshen Jihar Bayelsa ta dakatar da ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri da ɗan takarar gwamnan jihar a 2019, David Lyon saboda ayyukan zagon-ƙasa.

An kuma dakatar da wasu manyan jam’iyyar da suka haɗa da; Kwamishinan Lantarki, Kharim Kumoko; Kwamishinan filaye da safiyo, Peres Biewari; da tsohon shugaban jam’iyyar a jihar, Jothan Amos; da Godbless Diriwari, da kuma Shugaban matasan jam’iyyar reshen kudancin Ijaw, Sabi Morgan.

Sauran sun haɗa da; shugaban jam’iyyar a ƙaramar hukumar Ekeremor wanda Mitin Eniekenemi Senator ya sanar da hakan.

Eniekenemi Senator ya ce sun ɗauki matakin ne daga yanzu har zuwa lokacin da kwamitin ladabdtarwa zai yi hukunci game da su.