APC ta mayar da martani ga Amaechi, suna zargin shi da cin amanar jam’iyya

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta caccaki tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin da ta gabata kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, bisa zarginsa da tada zaune tsaye ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Amaechi a wata hira da yayi a baya-bayan nan ya caccaki matasan Nijeriya kan rashin yin zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a ƙasar.

Da yake mayar da martani ga jawabin a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Felix Morka ya fitar ranar Juma’a a Abuja, jam’iyyar mai mulki ta bayyana kalaman Amaechi a matsayin “rashin gaskiya da rashin kishin ƙasa.”

A cewar sanarwar, kalaman Amaechi ‘rashin hankali ne, abin ban tsoro ne kuma rashin kishin ƙasa, ya fito ne daga ɗaya daga cikin ‘yan Nijeriya da suka dade a kan karagar mulki.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Kusan duk tsawon rayuwarsa, Amaechi, ya kasance mai dogaro da dukiyar ƙasa, mai matuƙar cin gajiyar tallafin gwamnati, kuma babban mai taka rawa wajen lalata tattalin arzikin ƙasa.