APC ta cire Suswam da wasu daga jerin ‘yan takara na ƙarshe da ta tura wa INEC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyar APC ta cire tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswam, da wasu ‘yan takarar Sanata biyar daga jerin sunayen ‘yan takarar ƙarshe da ta miƙa wa Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC).

Haka kuma, jam’iyyar ta cire tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Ondo, Gbenga Elegbeleye, tare da maye gurbin wasu ‘yan takarar majalisar wakilai 19 da suka yi nasara a zaɓen fidda gwani na watan Mayun 2026.

A cikin wasiƙar da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ajibola Basiru, suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce sauye-sauyen sun biyo bayan rahoton Kwamitin Karɓar ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen fidda gwani.

Jihohin da sauye-sauyen suka shafa sun haɗa da Abia, Kogi, Taraba, Benue, Ebonyi, Ondo, Kaduna, Niger da Kwara.

Sai dai jam’iyyar ta tabbatar da sunayen wasu fitattun ‘yan takara da suka haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Mataimakinsa, Jibrin Barau; da gwamnoni AbdulRahman AbdulRazaƙ (Kwara), Hope Uzodimma (Imo), Ahmadu Fintiri (Adamawa) da Inuwa Yahaya (Gombe) domin fafatawa kujerun Sanata.

APC ta bayyana cewa ta karɓi sama da ƙorafe-ƙorafe 700 daga mambobinta kan zaɓen fidda gwani, tana mai cewa a halin yanzu fifikonta shi ne tabbatar da cewa duk ‘yan takara sun cike takardun tsayawa takara tare da loda su a manhajar INEC kafin wa’adin 10 ga Yulin 2026.

By ukarofi

Leave a Reply