Jam’iyyar APC mai mulki ta musanta zargin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, suka yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na bai wa wasu ‘yan adawa Naira miliyan 50 don tarwatsa jam’iyyun adawa a Najeriya, APC ta kira wannan zargi abun dariya marar tushe.
A wata sanarwa da sakataren yada labarai na APC, Felix Morka, ya fitar, jam’iyyar ta ce wannan zargi ba komai ba ne face ƙarya da ƙoƙarin jawo hankalin jama’a. APC ta bayyana cewa gazawar Atiku wajen tafiyar da jam’iyyarsa ta PDP ce ke haddasa rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta.
Har ila yau, APC ta yi watsi da maganganun Atiku da wasu jiga-jigan adawa da suka hada da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, da ke zargin cewa jam’iyyar mai mulki tana da hannu a rikicin da ke addabar jam’iyyun adawa. APC ta ce irin wadannan zarge-zarge alamu ne na gazawar ‘yan adawa wajen tafiyar da jam’iyyunsu, yayin da suka kasa daidaita matsalolinsu na cikin gida.
Jam’iyyar APC ta shawarci Atiku da sauran ‘yan adawa da su mayar da hankali kan gyara jam’iyyunsu maimakon yada jita-jita da bata suna. Ta kara da cewa dimokuraɗiyya ba kawai nasara a zaɓe ba ce, illa iyaka mutunta zaɓin jama’a da ƙokarin kawo cigaba ga ƙasa baki ɗaya.
