

Daga UMAR GARBA a Katsina
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) reshen jihar Katsina, ta sanar da janyewar mambobinta da ke aiki a wasu manyan asibitocin ƙananan hukumonin jihar Katsina da ke fama da rashin tsaro.
Shugaban ƙungiyar Mallam Nura Mu’azu ne ya bayyana haka lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Sakatariyar ƙungiyar dake Katsina.
A cewarsa, matakin da ƙungiyar ta ɗauka zai fara aiki ne daga tsakar daren ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, 2025 har sai gwamnatin jihar ta warware buƙatunsu.
Tattaunawar ƙungiyar na zuwa ne kwanaki 14 bayan da ‘yan bindiga suka sace ɗaya daga cikin mambobin mai suna Yusuf Mohammad Mai-Ruwa, wanda ake ganin yana ɗaya daga cikin nas-nas da suka fi nuna ƙwazo da ƙwarewa a fannin kiwon lafiya a jihar.
An sace ma’aikacin jinyar ne a lokacin da yake bakin aiki a babban asibitin Ƙanƙara a ranar Talata 15 ga watan Janairu, 2025.
Yayin da ta buƙaci a gaggauta samar da ingantaccen tsaro na tsawon sa’o’i 24 a dukkanin asibitocin da ke yankin da ‘yan bindinga suka fi kai hare-hare, ta ce wajibi ne hukumomi su ɗauki matakin gaggawa don ganin an sako ma’aikacin jinyar da sauran ma’aikatan lafiya da ɓarayin daji suka kama.
Kazalika, ƙungiyar ta bukaci a gaggauta biyan mambobinta da suka rasa rayukansu diyya a lokacin da suke bakin aiki, ta kuma buƙaci da a yi wa mambobin ƙungiyar ƙarin albashi don jawo hankalin jama’a su shiga aikin kula da lafiya domin samun ingantacciyar kiwon lafiya.
“Idan za ku iya tunawa, a ranar 15 ga watan Janairu,2025 mun rubuta wa Gwamnatin Jihar Katsina ta hannun hukumar kula da asibitoci tare da miƙa kwafin buƙatarmu a dukkan ofisoshin da abun ya shafa inda muka bayyana buƙatar samar da tsaro a asibitocin da ke fuskantar matsalar tsaro, sannan kuma muka bai wa gwamnati wa’adin sati biyu akan ta yi abun da ya dace ko kuma mu janye mambobinmu daga asibitocin Batsari, Ɗan-Musa, Ƙanƙara, Jibia, Dutsin-ma, Musawa, Malumfashi, Funtua, har ma da Ɓatagarawa.”
“Tun daga wannan lokacin gwamnati ta yi alƙawarin aiwatar da hakan a cikin kwanaki 3 zuwa 7 a waɗannan asibitoci.
“Abin takaici, makonni 2 ke cika amma ba a ga wani gagarumin yunƙuri daga gwamnati ba a zahiri duba da yadda matsalar ke rutsawa da mambobinmu ba za mu iya kawar da kai daga wannan lamari ba”, inji shugaban ƙungiyar.
