APC ta lashe zaɓen maye gurbi a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyu sun sha ƙasa a zaɓen maye gurbi na ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwaram da aka gudanar a jihar Jigawa ran Asabar da ta gabata.

Ɗan takarar jam’iyyar APC, Yusif Shitu Galanbi, ya samu nasarar lashe zaɓen ne inda ya yi nasarar a kan abokan hamayyarsa na PDP, Sharif Kamilu Maicalbi da sauransu.

Wannan shi ne karo na uku da Galanbi zai wakilci al’ummar yankinsu a Majalisar Wakilai ta Ƙasa.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Galanbi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Jami’in Hukumar Zaɓe da ya bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Ahmed Shehu, ya ce Galanbi (APC) ya doke Maicalbi (PDP) ne da ƙuri’u 29,372 bisa ƙuri’u 10,047.

Kamar yadda malamin zaɓen ya sanar, baki ɗaya yankin mutum 42,080 aka tantance don kaɗa ƙuri’a a lokqcin zaɓen, yayin da mutum 41,869 ne suka samu kaɗa ƙuri’a. Tare da cewa, an samu ƙuri’u 1,375 da suka lalace.

jami’in ya bayyana sakamakon da sauran jam’iyyu suka samu a zaɓen kamar haka: Jam’iyyar AA ta samu ƙuri’a 490, ADC ƙuri’a 44, APM ƙuri’a 57, APP ƙuri’a 18, NNPP ƙuri’a 26, NRM ƙuri’a 40, sai kuma PRP da ta samu ƙuri’a 366.

Ya ce kasancewar ɗantakarar APC shi ne ya fi samun yawan ƙuri’u, don haka Hukumar Zaɓe ta miƙa masa shaida a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 22 ga Maris, 2021 Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya tallata kujerar ɗan majalisar domin masu buƙata su nema biyo bayan rasuwar Hon. Yuguda Hassan Kila wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya a asibitin Abuja.