APC ta sauya lokutan fidda gwani na shugaban ƙasa da gwamnoni

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyya mai mulki APC, ta sanar da ɗage zaɓukan fidda gwani na shugabancin ƙasa da gwamnoni, tare da fitar da sabon jaddawalin gudanar da su.

A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an ɗage zaɓukan ne domin bai wa jam’iyya damar kammala shirye-shirye da gyare-gyare kafin gudanar da su cikin tsari mai kyau.

Jaddawalin ya nuna cewa za a fara sayar da fom daga ranar 28 ga Afrilu, 2026, sannan a rufe sayar da fom a ranar 10 ga Mayu, 2026.

Za a gudanar da ayyukan tantance ’yan takara daga ranar 14 zuwa 18 ga Mayu, tare da fitar da rahoton tantancewa a ranar 20 ga Mayu, 2026.

Haka kuma, jam’iyyar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna a ranar 24 ga Mayu, yayin da na shugaban ƙasa zai gudana a ranar 27 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta jaddada cewa wannan mataki ba zai kawo cikas ga shirye-shiryen babban zaɓen ƙasa ba, sai dai zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen tsari da adalci ga dukkan masu neman takara.

Matakin na zuwa ne yayin da harkokin siyasa ke ƙara zafi gabanin zaɓen 2027, inda jam’iyyu ke cigaba da tsara dabarun neman goyon bayan al’umma a sassan daban-daban na ƙasar.

By Babaji