MTN za ta biya kwastomomi diyya bisa rashin ingancin sabis

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewa zai bi umarnin Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) na biyan diyya ga masu amfani da layukansa da suka fuskanci matsalar rashin ingancin sabis.

A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, kamfanin ya ce duk kwastomomin da suka samu tangardar sadarwa a wasu yankuna za su ci gajiyar wannan diyya, musamman a lokutan da aka samu matsaloli a baya. Wannan ya biyo bayan matakin NCC na tilasta wa kamfanonin sadarwa su biya diyya idan sun kasa cika ka’idojin ingancin sabis (QoS).

Hukumar NCC ta jaddada cewa bai dace masu amfani su ɗauki nauyin gazawar sadarwa ba, don haka ta umarci kamfanoni su rika biyan diyya kai tsaye. An ce diyya za ta kasance ne ta hanyar ƙarin airtime ko data, kuma za a tantance ta bisa yadda mai amfani ke kashe kuɗi da kuma yankin da matsalar ta shafa.

Haka kuma, an bayyana cewa masu amfani ba sai sun nemi diyya ba, domin kamfanonin sadarwa za su gano waɗanda abin ya shafa su biya su kai tsaye. Wannan mataki zai shafi matsaloli irin su yankewar kira, sakonni da ba sa isa, da kuma tangardar data.

A ƙarshe, MTN ta ce tana ƙara zuba jari domin inganta hanyoyin sadarwarta, tare da ƙarfafa kayan aiki da rage irin waɗannan matsaloli a nan gaba.

By Babaji