
Daga BELLO A. BABAJI
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta tabbatar da batun shigarta zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 24 ga watan Oktoba a jihar.
Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas ya bayyana hakan wa jaridar ‘News Agency Nigeria’ a yayin wata ganawa a ranar Alhamis inda ya ce nan ba da jimawa ba za su yi zaɓen fidda gwani, ya na mai bayyana damarsu ta cin nasara a zaɓen.
Ya ce, a halin yanzu jami’yyar tana ƙoƙarin haɗe kan mambobinta na ƙananan hukumomi 44 da ke jihar don samun babban gurbi a zaɓen.
Ya kuma ce, jihar Kano ta na da tarihi mai ƙarfi game da siyasa wanda jam’iyyarsu a shirye ta ke ta yi galaba a zaɓen.
Abbas ya yi kira ga hukumar zaɓe ta jihar ta tabbatar da an gudanar da zaɓukan cikin tsari da adalci ta yadda jama’a za su samu gamsuwa.
Hakan na zuwa ne yayin da APC ke shirye-shirye fafatawa a zaɓen da ke tafe musamman ga babbar abokiyar adawarta ta NNPP da ke mulki a jihar.
