
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an tsaro na al’umma (Civil Defence), sun yi nasarar kama wani matashi ɗan hidimar ƙasa mai suna Tayana Rambson ɗan asalin jihar Adamawa da fasa wani gida a rukunin gidajen Sarki Muhammad Sarki a garin Katsina.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, DSC Buhari Hamisu ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da ya ke gabatar da wanda ake zargin inda ya ke ɗauke da kayan satar.
Ya ce, wanda ake zargin ya fasa wani gida ne a rukunin gidajen inda ya kwashe duk kayan da ke gidan har da wayoyin lantarkin gidan ya tsitstsinke waɗanda su ma ya yi awon gaba dasu .
DSC Buhari ya bayyana cewa, jami’an nasu sanadiyyar sintiri da suke gudanarwa ne, sai suka rutsa da shi cikin dare da waɗannan kayayyakin da ya sata a wani lungun gidajen.
Sai dai, ko da ganin sun dunfaresa sai ya fidda wuƙa ya na ƙoƙarin kai mu su hari har ya jima ɗaya daga cikin su rauni, amma duk da haka sun samu nasarar kama shi.
An same shi da kayan gidan da ya sata kala-kala har guda 35 da suka haɗa da kayan ɗakin dafa abinci da kayan ɗakin kwana, talabijin da fankoki da sauran su
Wanda ake zargin ɗan asalin ƙauyen Kwakwa’ah ne a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa ya amsa laifinsa har ya ƙara bayyana cewa kwanaki kaɗan kafin wannan satar, ya shiga wani gidan inda a nan ma ya yi sata.
Ɗan hidimar ƙasar wanda ya yi karatunsa a jami’ar Maiduguri, ya yi digirinsa a fannin namun daji don haka ya ke hidima a gidan namun dajin ‘Aldusar Zoo Park’ a cikin garin Katsina.
DSC Buhari ya kuma ce, da zarar sun kammala bincike, zasu gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.
Kwamandan rundunar na jihar, Jamilu Abdu Indabawa, ya yaba wa jami’ansa kan namijin koƙarin da suka nuna wajen kama wannan ɓata-gari.
Ya nuna takaicinsa na ganin yadda ɗan bautar ƙasar da wanda bai rasa ci ko sha ba ya ɓata rayuwarsa.
