



Daga Sanusi Muhammad a Gusau
Rundunar Sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan ta’adda da aka sani da Kachalla Halilu a wani artabu da suka yi a kan babbar hanyar Sokoto zuwa Gusau a ranar Juma’a.
Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ziyara a ofishinsa, ranar Juma’a.
Janar Musa ya shaida wa gwamnan cewa an kashe Kachalla Halilu da mabiyansa da dama a yayin fafatawar.
Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Kachalla Halilu tare da mabiyansa sun halarci wani taro ne da ɗan bindigar nan Bello Turji a sansaninsa su fiye da dari, yayin da sojoji suka yi musu kwanton ɓauna a kauyen Mayanci na ƙaramar hukumar Maru a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa, Kachalla Halilu ya addabi yankin Zamfara ta yamma da ya haɗa da; Kaura Namoda, Shinkafi, Birnin Magaji da Zurmi a Zamfara.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, sojoji sun kuma kashe ƴan bindiga sama da 100 a yayin fafatawar, inda aka kuma samu nasarar ƙwato babura da makamai da kuma harsasai masu yawa a yayin musayar wutar da rundunar sojin Wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i ana yi.
Manhaja ta kuma ruwaito cewa, titin gwamnatin tarayya da ya haɗa Gusau zuwa Funtua da Gusau zuwa Sokoto, ya zama tarkon mutuwa sakamakon yawaitan ayyukan ƴan bindiga da suka addabi matafiya kusan kullum.
