Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da tallafa wa waɗanda ambaliya ta rutsa da su – Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya nanata ƙoƙarin gwamnatin tarayya na cigaba da tallafa wa waɗanda ambaliya da halin rashin tsaro suka rutsa da su, ya na mai cewa za ta ƙara kayayyakin tallafi ga jihohin da lamuran suka shafa.

Ya ce, gwamnatin tarayya da na jihohi tare da hukumar bada agaji ta gaggawa (NEMA) suna aiki tuƙuru don faɗaɗa bada taimako ga yankunan.

A yayin ziyararsa a sansanin ƴan gudun hijira da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja a ranar Juma’a, Shettima ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta na cigaba da mayar da hankali wajen shugabanci mai inganci da kula da ƴan Nijeriya sama da yadda ake tsammani a siyasance.

Cikin wata takarda da mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha ya fitar, Shettima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na cigaba ƙoƙarin warware matsalolin abinci da rashin tsaro da ke addabar yankin.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce, a kwanakin baya ne gwamnatin tarayyar ta bai wa kowacce jiha Naira biliyan 3 don rage raɗaɗin matsalolin ambaliya.

By Babaji