Arewa ku farka, ku tashi ku tabbatar da muradun yankinku – Abdulaziz Bako

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da Majalisar Dokokin Nijeriya ke ci gaba da nazarin sauye-sauye fiye da 80 cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, yankin Arewa na ci gaba da zama cikin shiru da rashin damuwa. Sauye-sauyen da ka iya gurgunta tattalin arziki, zamantakewa da siyasar yankin, saidai abin takaici suna ƙoƙarin wucewa cikin shiru.

A cewar wani mai rajin kare muradun Arewa, Abdulaziz Bako, mafi yawan sauye-sauyen na da illa kai tsaye ga Arewa. “Wannan ba magana ce ta jam’iyya ko ƙabila ba, magana ce ta makomar yanki gaba ɗaya,” inji shi.

Daga cikin batutuwan da ya fi tsorata da su akwai:

Rikicin VAT 50% derivation, wanda zai bar Arewa cikin talauci.

Ikon sarrafa albarkatu: Jihohin mai su ci 75%, sauran su bar 25% kawai.

Shiga indigeneship bayan shekaru 10: wanda zai sauya fasalin amfani da tsarin kwadago da wakilci.

Kafa kotunan Kiristoci: wanda ke iya tayar da sabbin muhawara a ɓangaren shari’a.

Ya ce: “Wannan sauyi ba ɗan sauyi ba ne, an gina shi ne don karya sashen Arewa da ƙarfafa kudanci. Lokaci ya yi da za mu tashi tsaye.”

By ukarofi