A baya-bayan nan Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Mohamed Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama ƙwayoyin Tramadol biliyan 1.3 da kwalaben Codeine miliyan 4.4 tsakanin watan Janairun 2024 zuwa Yunin 2025.
Marwa ya bayyana hakan ne a yayin wani zama na musamman a taron tattaunawa na kwana biyu kan haɗin gwiwar gwamnati da ’yan ƙasa da aka yi ranar Talata a Kaduna.
Ya kuma yaba da irin gagarumin nasarorin da aka samu ga tallafin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya baiwa hukumar.
“Tsakanin Janairu 2024 zuwa Yuni 2025, mun kama sama da kwalaben codeine miliyan 4.4. Mun kuma kama allunan opium biliyan 1.3 da aka fi sani da tramadol. Taramadol guda ɗaya a yanzu ya kai Naira 1000. Adadin kuɗin ƙwayoyin biliyan ɗaya zai iya kaiwa kusan naira tiriliyan ɗaya.
“Ku yi tunanin irin makaman da ‘yan ta’adda ko ‘yan fashi za su iya saya da wannan adadin ko kuma ku yi tunanin kwayar tramadol biliyan ɗaya da ke yaɗuwa,” inji shi.
A cewar Marwa, tun lokacin da Tinubu ya hau kan karagar mulki a shekarar 2023, hukumar ta kwace muggan ƙwayoyin guda 5,555, kwatankwacin tireloli 200.
Ya ce, “Ku yi tunanin tireloli 200 na haramtattun abubuwa a kan titunan mu. Haka kuma, mun kama masu fataucin miyagun ƙwayoyi 2000, mun yanke wa 8,682 hukunci, sannan muka gyara sama da 24,000.
“Muna kuma ci gaba da bayar da shawarwari ga wuraren shaƙatawa, makarantu, coci-coci, masallatai, kasuwanni, da dai sauransu don wayar da kan jama’a game da illolin muggan ƙwayoyi da shaye-shayen ƙwayoyi. Duk waɗannan ya yiwu ne tare da goyon bayan Tinubu.”
Akan ba da shawara da gyara, shugaban NDLEA ya bayyana cewa Tinubu ya amince da gina cibiyoyi bakwai na hukumar.
Wani abin sha’awa, hukumar ta kai yaƙi da miyagun ƙwayoyi zuwa ƙofar masu noman taɓar wiwi ta hanyar lalata gonakin taɓar mai fazin hekta 772.5. A cikin watanni 22, ta hukunta sama da mutum 3,434.
ɗaya daga cikin illar shan muggan ƙwayoyi shine haifar da matsalar tsaro. A halin yanzu an ɗora Nijeriya a matsayin ƙasar da ta fi hatsari a kan ayyukan ’yan ta’adda. A bin takaicin shi ne yadda harkokin ’yan ta’adda ke ƙara ƙaruwa a kullum suna cin karen su babu babbaka, duk da cewa, babu wani sashe na duniya da ya tsira daga abubuwan da suka shafi ayyukan ’yan ta’adda amma lamarin Nijeriya yana da ban tsoro.
Don nuna jajircewarsa a kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi, shugaban ƙasa Bola Tinubu a shekarar da ta gabata ya ƙaddamar da shiri na musamman da aka yi wa laƙabi da ‘War Against Drug Abuse” (WADA)’ da kuma kundi na musanmman mai suna “National Drug Control Master Plan 2021-2025” na yadda za a fuskanci yaƙi da miyagun ƙwayoyi a sasan ƙasar nan.
Shugaban ƙasar ya kuma ce, barazanar da miyagun kwayo ke yi wa kasar nan ya fi na ayyukan ta’addanci da ake fuskanta.
Mun amince da bayanin shugaban ƙasa na cewa, miyagun ƙwayoyi ya taimaka wajen ƙara zafafa ayyukan masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda a sassan Nijeriya, mun kuma amince da irin nasarorin da NDLEA ke samu a yaƙi da miyagun ƙwayoyi, muna kuma kira da a kara ƙaimi wajen zafafa yaƙin da ake yi da masu safara da mu’amala da miyagun ƙwayoyi a sassan ƙasar nan ta haka za a tabbatar da rage lamarin yadda ya kamata.
Wannan yaƙi na kowa da kowa ne a saboda haka muna kira ga iyalai, makarantu da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran al’umma gaba daya su kawo nasu gudummawar don samun nasarar fatattakar masu safarar ƙwayoyi da masu mu’amala da ita, tare da kuma ba hukumar NDLEA goyon bayan da take buƙata gaba ɗaya.
Babu shakka, shawarar da mahukuntan hukumar suka yi na yin amfani da na’urorin wajen inganta martabar hukumar na iya haifar da gagarumar rawar da hukumar ta taka. Don haka ne hukumar NDLEA ƙarƙashin jagorancin Marwa ta ƙuduri aniyar yin duk mai yiwuwa don inganta ayyukan da ake yi. A bara, NDLEA ta ƙara wa jami’ai 3,506 karin girma. A bana, an ƙara wa jimillar jami’ai 1,018 ƙarin girma zuwa sabbin mukamai.
Marwa ya yi amfani da wannan dama wajen yabon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda irin goyon bayan da yake bai wa hukumar ya sa hukumar ta samu nasara a aikin da ya ba ta. A yayin da muke yabawa Shugaba Tinubu kan ƙudirin kawar da miyagun ƙwayoyi a ƙasar nan, muna roƙonsa da ya fitar da miliyoyin ’yan Nijeriya daga ƙangin talauci ta hanyar samar da ayyukan yi masu yawa da sauran matakan rage raɗaɗin talauci.
Mun faɗi haka ne saboda akwai wata alaƙar da ba za a iya raba ta ba tsakanin ƙaruwar talauci a ƙasar da ƙaruwar amfani da muggan ƙwayoyi. Muna kira ga al’umma da su guji ta’ammali da muggan ƙwayoyi domin gujewa faɗawa aikata laifuka.
