Ashe jami’an lafiya 400,000 ne a Nijeriya

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Lafiya uwar jiki inji masu iya magana inda har su ka ƙarasa da cewa babu mai fushi da ke. A gaskiya yawancin mu ba za mu fahimci muhimmancin kiwon lafiya ba sai in mun samu ƙalubalen rashin lafiya. Ba ma nan matsalar ta ke ba sai lokacin da mutum ya samu matsalar rashin lafiya ya ruga asibiti zai gane ashe ba sauƙi lamarin ya ke da shi ba.

Wato mutum ya samu likita ya duba shi don a rubuta ma sa magani da zai shiga shagon sayen magani ya saya da kuɗin sa ma aiki ne. Kuma ai akasarin talakawa kan asibitocin gwamnati su ka dogara. Kuma yaushe ne a ka tava samun dogon lokaci a Nijeriya likitoci ba su tafi yajin aiki ba. Za ka ga je asibiti don a gaggauta duba ka don kar matsala ta ta’azzara sai kawai ka tarar an fi yajin aiki. In kuma ka leƙa asibitin kuɗi za ka tarar hatta kudin gado ma in ta kama a kwantar da kai ba za ka iya biya ba.

Ni na ga asibitin kuɗin da sai marar lafiya ya zauna ya jira likita an buga waya can bayan mutum ya fara galabaita sai ya zo ya duba kuma ba lalle ne ma a samu biyan buqata ba. Kuma likitocin fa da ke zama a asibitocin kuɗin su ne na asibitocin gwamnatin. Likita ya yi aiki a asibitin gwamnati in an buga ma sa waya a asibitin kuɗi sai ya tafi can ya yi aiki.

Haƙiƙa wannan ba wani baƙon abu ba ne ga duk wanda ya samu jinya. Da yawa mutane na tafiya da cuta a jikin su don sanin in sun je asibiti sai yadda hali ya yi. Abun da a ke gudu shi ke faruwa wato mutane su riƙa shiga dakunan sayar da magani su na sayan maganin da su ke tsammani shi zai yi mu su aiki ba tare da sun samu likita ya duba su an tabbatar da abun da ke damun su ba. Wasu da dama daga jama’a musamman talakawa sun zama likitocin kan su.

In ka ga wani ya dage sai likita ya duba shi to ciwo ya kai matsayin da ba yadda zai iya cigaba da shayar da kan sa magani. Wani ma sai in ya zama sai a kwantar sai a tayar sannan ne za a garzayo da shi asibiti don duba shi. Kazalika zai iya yiwuwa ma wasu kan shiga asibitocin da ba na ƙwarrau ba ko kuma su riƙa karvar maganin daga likitoci masu yawo kan tituna da jakar magani a hannu. Ni na tava ganin wani ya na yin allura da ba da magani a tashar mota.

Da zarar wani ya ce ba shi da lafiya sai a ce a kira dokta ya duba shi. Wannan na nuna mutane kan zaɓi kula da kan su ga cutar da ba ta hana su fita neman na cefane. Wani ma za ka ji har bugun ƙirji ya ke yi cewa shi a tsaye ya ke maganin ciwo don ba a ma taba kwantar da shi a asibiti ba. Haƙiƙa akwai buƙatar gyara ne a kowane ɓangare kama daga mutanen kan su, likitoci da kuma uwa uba gwamnati.

Duk maid an sukuni za ka tarar burin sa in ya samu ƙalubalen rashin lafiya ya nemi izinin fita turai ko Indiya don neman magani. Wasu ma Masar a nan Afurka ta arewa su ke tafiya don a duba su. Wani labarin da na samu shi ne a can ƙasashen wajen ma mutum kan iya zuwa sai ya gamu da likita ɗan Nijeriya ya duba shi. Ya zama mai muhimmanci gwamnatoci a dukkan matakai su maida hankali kan lamarin kiwon lafiya.

Idan al’umma ta zama ba lafiya to ba wani cigaba mai ma’ana da za a iya samu. Abun da zan ƙarfafa a nan shi ne ko gwamnati za ta cire tallafi a kowane ɓangare to ta dawo da tallafin ɓangaren kiwon lafiya. In mu ka kawo batun abinci, to shi ma ai sai da lafiya za a nema. Ga jihohi musamman da ƙananan hukumomi ke ƙarƙashin su, ya dace su riƙa shake asibitoci da magunguna ba wai kawai sabon gini ko fenti ba.

Idan talaka majinyaci ya shiga asibiti mai kyau amma ba likita ko ba magani ai ya zama aikin baban giwa. Kuma yawanci za ka samu ga asibiti an gyara an shuka bishiyi an ma saka gadaje da masu gadi amma ɓangaren magani sai dai in mutum ya na da kuɗi.

Babban ministan lafiya na Nijeriya Dr.Muhammad Ali Pate ya ce akwai sama da likitoci da sauran jami’an lafiya sama da 400,000 a Nijeriya amma ba su wadatar ba don haka akwai buqatar kari. Ministan ya ce in an duba yawan ’yan Nijeriya fiye da mutum miliyan 200 to likitoci da sauran duk ma’aikatan lafiya 400,000 sun yi kaɗan ainun wajen kulawa da buƙatar kiwon lafiyar waɗannan mutane masu yawan gaske. Kazalika a kullum a kan samu ƙaruwar mutane da yawan vullar cututtuka.

Muhammad Pate ya nuna shirin shawo kan hankalin ƙwararrun likitocin Nijeriya a ketare su riqa waiwayowa don taimakawa lamuran jinya a cikin gida.

Ministan wanda ya ke magana a karo na farko bayan amsar madafun iko da ganawa da dukkan sassan ma’aikatar lafiyan, ya ce haƙiƙa akwai jami’an lafiya musamman a yankunan karkara da ke faɗi-tashin kula da majinyata kuma su na buƙatar a ba su kwarin guiwar yin hidima ga ƙasa. Jami’an na aiki ba tare da wadatar kayan aiki ko samun ihsanin ƙwarin gwiwar yin aikin ko tabbatar da tura su kwas don ƙara ƙwarewa kan aiki ba. Wasu ma na buƙatar karo ilimi a jami’o’i don dawowa su kula da al’umma don kar aikin wasu ya zama ’yan gyara sa’a.

A nan ministan ya nuna damuwa cewa kimanin kashi 90% ko fiye na magunguna da sauran kayan jinya da a ke amfani da su a Nijeriya daga waje a ke shigo da su, don haka za a buɗa tsarin da za a riƙa samar da su a cikin gida. Ministan ya ce a kan shigo da magunguna daga ma wasu ƙasashen da ba su kai Nijeriya tasiri a duniya ba. Wani misalin ma shi ne hatta gadaje da a ke kwantar majinyatan a kan shigo da su daga waje ne alhali Nijeriya na da ƙwararru da za su iya ƙera gadajen da sauran kayan aiki in an ba su dama.

Hakanan ministan ya nuna muhimmancin masu magungunan gargajiya da ya ce za a neme su a gudanar da bincike kan irin magungunan su don gano masu tasiri da za a sanya a tsarin kiwon lafiya don agazawa jama’a musamman a karkara. Don an ji gargajiya ba ya na nufin magunguna na qauye ba ne don ministan ya ce a Turai ma a na amfani da magungunan sayu da kauci don taimakon kiwon lafiyar jama’a.

Minista Pate ya yi alwashin bin dukkan hanyoyin shawo kan likitoci su daina tafiya yajin aiki don ceton marar sa galihu. A nan ministan bai kawo batun ƙarin albashi ba sai dai ya nuna alamun neman cusawa likitoci kishin kasa don aikin kiwon lafiya tamkar wata gudunmawa ga jama’a da mai ilimin zai yi don samun lada na taimakon sauran ’yan uwa. Dr. Pate ya ce ai bai dace don likita ya na da ƙorafi mace ta zo haihuwa jini ya tsinke ma ta sai ya ƙi kula da ita har hakan ya iya sanadiyyar ran ta ba.

Ministan ya gudanar da zaman ganawa da manema labaru da ƙaramin ministan lafiya Dr.Tunji Alausa wanda ya maida hankalin kan amfani da adana bayanai majinyata a na’ura don sauƙaƙa ba da kulawa a ko’ina. Tattara bayanin marar lafiya a waje ɗaya na da amfani da zai dakatar da dogon bincike kafin wani likitan ya duba majinyaci.

“Za mu maida hankali wajen tara bayanan majinyaci don haka in ya shiga wannan asibiti a wannan gari to gobe in ya shiga asibitin a wani gari sai kawai a duba na’ura a ga bayanan don cigaba da kulawa da shi”

Ficewar kwararrun likitoci daga Nijeriya zuwa ƙetare don samun albashi mai kyau na daga ƙalubalen kiwon lafiya a Nijeriya; inda ministan ya ce akwai boyaiyun kwararru a cikin gida da za a fito da su fili don mutane su riqa amfana da kwarewar su. Pate ya ce ya san akwai masana kiwon lafiya a sassan Nijeriya da ba su yi fice ba, don haka mutane ka iya tsallake su su fice ketare; don haka za a zaƙulo su don mutane su san su da kuma amfana da baiwar da su ke da ita

Kammalawa;

Komai sai da lafiya a ke iya gudanar da shi. Kowa ya riƙa kula da yadda ya ke ji a jikin sa don ɗaukar mataki ba sai an kai matsayin ba za a iya motsawa sai da taimakon ’yan uwa ba. Ciwon kai ko zafin ƙirji da samun kasala na daga alamun wasu cutukan da ke buƙatar a ga likita fiye da dabarar sayen “PARACETAMOL” a dan ji sauki shikenan sai in an sake jin baya ya cike ko kafa ba ta son hawa matakalar bene.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *