Asibitin ƙwararru na Bauchi da ke Bacas na fuskantar ƙalubale saboda arahar adana gawa

Spread the love

Daga MUAZU HARɗAWA a Bauchi

Ganin yadda ake da sauƙin farashin adana gawarwakin mutanen da suka rasu a asibitin ƙwararru na Bauchi da ke Bacas, hukumar asibitin ta bayyana irin ƙalubale da take fuskanta saboda lalacewar na’urorin sanyi na asibitin a halin yanzu.

Farfesa Mairiga Abdulkarim CMD wato shugaban asibitin shine ya bayyana haka cikin hirarsa da manema labarai a ofishin sa. Don haka ya ƙara da cewa a asibitin ƙwararrun na Bauchi suna da firjiin na’urarr sanyi da ake ajiye gawa guda 20 a asibitin, amma 18 daga ciki sun lalace, sauran guda biyu da suka rage kuma basa aikin da ya dace idan an sa gawa a cikin sanyin baya gamsarwa daga bisani gawar tana lalacewa kwana kadan take fara wari daga waje ana ji.

Don haka ya ce hakan na haifar da matsala saboda da rashin sanyin yana hana gawa tsantsamewa, don haka gawar mutane tana ruɓewa tana wari.

Ganin haka suka daina karɓar gawar da ake kawowa saboda wasu ‘yan uwan suna kawo ajiye gawa su ce zuwa gobe daga bisani su ɗauke ƙafa a rasa yadda za a yi da gawar har ta fara damun asibitin da wari.

Dr. Abdulkarim Garba Mairiga ya ƙara da cewa sun ɗauki wannan mataki ne don kare lafiyar rayayyu da tsabtar asibitin. 

Musamman ganin Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi ya bayar da kwangilar gyaran asibitin wanda nan ba da jimawa ba za a fara aikin, kuma za a gama cikin wata shida.

 ɗakin adana gawarwakin wato motuary yana cikin wuraren da za a gyara, kuma dukkan firiji 20 za a gyara su, kuma da zarar an dawo cikin asibitin za a fara aiki da su a ci gaba da karbar gawarwakin mutane da ke bukatar ajiyewa ana adana musu.

Bincike da muka gudanar mun gano sauƙin ajiye gawa da gyara ko wanke gawa a asibitin na BACAS yadda ake karɓar naira dubu biyu kwana ɗaya shine ya sa wasu mutane musamnan ƙabilu sukan kawo ajiye gawa kafin daga bisani idan sun shirya jana’iza irin ta al’ada sukan ɗauka su tafi da su garuruwansu don bisnewa.

Amma a asibitin koyarwa na ATBUTH kowane kwana guda da gawa za ta yi a firji ana biyan naira dubu bakwai ne kuma a biya kuɗin gyara gawa, don haka mutane ke son kawowa asibitin ƙwararru na Bauchi.

Farfesa Mairiga Abdulkarim ya ba mutane haƙuri kan lamarin, saboda idan sun karɓi gawa ba a zuwa a ɗauka a kan lokaci lamarin yana zama damuwa. Musamnan a wasu lokuta jami’an tsaro suna kawo gawa amma bincike don neman masu gawar yakan ɗauki lokaci a barsu da gawa babu mai ita har ta fara wari, kuma bisa doka ba za su bisne ba sai an ba su izini. Yin sutura wa gawar shima sai sun kashe kuɗin likkafani da rami da abin hawa da sauran ɗawainiya.

Bayan haka idan kuma suna aiki da firji guda biyu don adana gawa biyu idan wasu sun kawo an ce ba wuri mai kyau shi ma mutane suna ɓata rai, wani lokacin har su ga kamar an ƙi karɓa ne da gangan.

Ya ce kusan sau uku ana kawo musu gawarwakin daga jami’an tsaro amma rashin aikin wajen ajiye gawar ya sa suka fara wari kusan ta ko’ina aka fito ana jin wari, don haka suka buƙaci su ba su izini a musu janaza suka ki kuma suka ki zuwa suka ce suna binciken lamarin har ya kai ga an samu sabani suka ce za su dawo musu da gawar ofishin jami’an tsaron don ba za su bari mutane su cutu ba kafin daga karshe suka ba su izini suka yi wa gawar janazar.

Amma ya buƙaci mutane su ci gaba da kai ajiye gawarwakin zuwa asibitin koyarwa kafin a gama aikin gyaran asibitin wanda da za a fara nan ba da jimawa ba.

By ukarofi