’Yan Boko Haram sun harbe kyaftin ɗin sojoji a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan ta’addan Boko Haram sun kashe wani kyaftin na sojojin Nijeriya a ƙauyen Izge da ke ƙaramar Hukumar Gwoza, a Jihar Borno.

Manhaja ta rawaito cewa rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun kai harin ne da safiyar Laraba, inda suka kashe kyaftin ɗin tare da wani soja guda.

Mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun iso yankin da misalin ƙarfe 1:00 na dare suka fara musayar wuta da dakarun sojoji.

“Gaskiya ne cewa al’ummata a Izge sun fuskanci hari daga ‘yan Boko Haram da misalin ƙarfe 1:00 na dare. Abin takaici, Kyaftin ɗaya da soja ɗaya sun rasa rayukansu.

“Amma dakarunmu masu jarumta na JTF na farar hula, masu farauta, masu gadi da kuma al’ummar yankin masu ƙwazo sun kashe ‘yan ta’adda uku. ‘Yan ta’addan sun bar makamai, babura sama da goma,” inji shi.

By ukarofi