Haɗaka: Ba na buƙatar amincewar ’yan jagaliyar siyasa – Martanin Atiku ga Bwala

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma jagoran adawa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta firgita da yunƙurin da suke yi ƙulla haɗakar jam’iyyun adawa.

Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga kalaman Daniel Bwala, tsohon hadiminsa kuma mai bai wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, inda ya shawarci Atiku da ya haƙura da takara a zaɓen 2027.

Cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, Bwala ya ce: “Ya kamata Atiku ya yarda da ƙaddara, wataƙila ba nufin Allah ba ne ya shugabanci Nijeriya.”

A martanin da ya fito daga ofishin yaɗa labaran Atiku, an siffanta kalaman Bwala da “raini da kuma rashin mutunci.

“Ceto da gina Nijeriya aikin ne mai matuƙar muhimmanci na ƙasa, wanda bai kamata a bar shi yana tangal-tangal ba saboda son zuciyar wasu hadiman fadar shugaban ƙasa masu neman faranta wa kansu rai,” inji sanarwar.

By ukarofi