ASUP ta janye yajin aikin kwanaki 65

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha (ASUP), ta janye yajin aikin da ta shafe kwanaki 65 tana yi don bai wa gwamnati damar yin abin da ya kamata.


Sanarwar da ASUP ɗin ta fitar a Laraba ta hannun sakatarenta na ƙasa, Comrade Abdullahi Yalwa, ta nuna cewa, “Bayan samun rahoton gwamnati ta soma aiwatar da buƙatun da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnatin tarayya, ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 65 tana yi daga ranar 10 ga Yunin 2021.”

ASUP ta ce “Dakatarwar ta watanni uku ne kawai domin bai wa gwamnati zarafin kammala buƙatun da ke tattare cikin yarjejeniyar da aka sanya wa hannu tare da ƙungiyar tun 27 ga Afrilu, 2921.

“A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi, Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ta ce ta yi nasarar kammala wasu ayyuka kamar sabuntawa da kuma kafa kwamitin gudanarwa da majalisar sanya ido a Kwalejojin Fasaha na Tarayya, yayin da a yanzu haka ana kan duba batun ariyas na mafi ƙarancin albashi da yadda za a bada kuɗaɗe don aikin samar da gine-gine.

“Sauran abubuwan sun haɗa da ƙoƙarin nazarin tsarin aiki da dokokin aiki na makarantun da kuma batun alawus na CONTISS 15 ga ƙananan ma’aikata.

“Sai kuma batun nan na samuwar dokar da ta cire mambanci ga shaidar karatu ta HND a ƙasa.”

Ƙungiyar ta ce kafin cimma shawarar janye yakin aikin, sai da ta yi la’akari da roƙon da gwamanati, sarakunan gargajiya, ‘yan Majalisar Tarayya, al’ummar ƙasa da sauransu suka yi mata.

Malaman sun ce suna fata janye yajin aiki zai bai wa gwamnati damar cika sauran buƙatun nasu kamar yadda suke ƙunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma. Tare da nuna godiyarsu ga dukkanin waɗanda suka nuna damuwarsu wajen ganin an samu maslaha.