Dambo ya zama shugaban Hukumar Alhazai ta Zamfara

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya naɗa Abubakar Sarkin-Pawa Dambo a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar.

Naɗin Alhaji Dambo na daga cikin sabbin naɗe-naɗen da gwamnan ya yi a makon jiya.

Sanarwar naɗin ta bayyana ne a Talatar da ta gabata cikin wata sanarwar da ta samu sa hannun muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Kabiru Balarabe.

Alhaji Sarkin-Pawa Dambo shi ne shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Alhazai Musulmi na Jihohi.

Kazalika, sanarwar ta sake nuna naɗin da aka yi wa Sheikh Abubakar Muhammad Sodangi Gusaua a matsayin Sugaban Hukumar Zakka da Taimako na Jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *