Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Duk sa’o’in Atiku Abubakar a siyasa, ko dai sun kwanta dama, ko sun yi ritaya daga siyasa. Kada mu manta Atiku Abubakar ya fara takarar shugaban kasa tun a shekarar 1993, shekaru 33 da suka gabata. Atiku ya yi gwagwarmayar siyasa da irinsu MKO Abiola, Shehu Yar Adua, Adamu Ciroma, Abubakar Rimi, Bashir Tofa, Babagana Kingibe da sauransu.
A tsawon wannan gwagwarmaya tasa, sau uku ya sami cikakkiyar damar zama shugaban kasar Najeriya. Na farko a 1993 amma maslaha ta cikin gida ta sa aka ba shi hakuri ya janyewa Abiola. Bayan ya zama mataimakin shugaban kasa, 1999-2003, bai taba samun dama irin a wannan lokaci ba, saboda ya zama Dan siyasa Mafi karfin fada a ji, musamman daf da zaben 2003. Gwamnoni sama da 20 da daruruwan Yan majalisa da kuma shugabannin PDP a wancan lokaci sun ba shi goyon baya.
Hankalin Obasanjo ya yi matukar tashi sakamakon barazanar Atiku, kamar yadda wani tsohon Sanata ya shaida min, wanda da shi aka yi, ya ce wasu gwamnoni da sanatoci da yan majalisar tarayya da shugabannin PDP sun halarci Taron gaggawa a gidan Atiku daf da zaben 2003. Bukatar su ita ce Atikun ya ayyana cewa zai yi takarar shugaban kasa a PDP. Ana tsaka da wannan taro sai Obasanjo ya fado gidan, inda su ka haye saman bene su ka yi wata doguwar ganawa. Wasu majiyoyi sun ce har sai da Obasanjo ya yi wa Atiku “dubale” domin ya hakura ya janye takararsa ya goyawa Obasanjo baya, da alkawarin zai bashi takara a 2007.
Me ya kamata Atiku ya yi? A cewar wannan Sanata sai kawai Atiku ya sauko tare da Obasanjo ya sanarwa wadannan mutane da ke hankoron ya tsaya takara cewa sun daidaita da Obasanjo, kuma ya janye takararsa, ba tare da neman yardarsu ba. Wannan bayani ya batawa mutane da dama Rai wadanda su ka halarci taron, yadda shi wannan Sanata ya ce, daga ranar ya san Atiku ba zai zama shugaban Najeriya ba kuma ya daina goyon bayansa.
A shekarar 2023, wato shekaru 20 kenan cif bayan waccan neman takara, Atiku ya sami babbar damar da bai taba samu ba a muradinsa na zama shugaban Najeriya. Dalili kuwa shine, ya sami takara a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma sakamakon mulki karo biyu a jere na Muhammadu Buhari karkashin APC ya lalata komai a kasar yadda babu komai sai talauci da wahala ga talaka sannan cin hanci da rashawa ya mamaye ko’ina baya ga matsalolin rashin tsaro na ta’addanci, satar mutane da mahara yan bandits. Sakamakon kuri’u sama da miliyan 16 da ilahirin Yan adawa su ka kada, ya tabbatar da cewa hakika yan Najeriya sun gaji da mulkin kama karya na APC karkashin Buhari. Amma sakamakon rashin lissafin da Atiku ya nuna ya janyo nasarar jam’iyya Mai mulki lashe zaben da kuri’a miliyan 8 kacal.
A 2019, Atiku ya yi takara da Peter Obi amma ya sake Obi ya balle a 2023. Taurin kai mara tushe, ya sa Atiku ya ki amincewa da sauke Ayu daga shugaban jam’iyya kamar yadda su Wike su ka nema, babbar illa da ta kassara PDP, kuma Wike ya fada tarkon APC. Abin takaici kuma shine, wata shida kacal bayan faduwa zaben Ayu ya yi murabus, abinda Atikun ya ki amincewa da shi kafin zabe. Duk mai lissafi zai gane cewa Atiku ne ya kada kansa da kansa a 2023.
Tun bayan zaben 2023, APC ta gane babban hadarin da ta tsallake a 2023, don haka su ka sake zage dantse wajen tabbatar da cewa, nasararsu ita ce ci gaba da makure yan adawa da kawo musu cikas wajen haduwa waje guda. Tashin farko sai suka baiwa Wike mukamin minister mafi mahimmanci na Abuja, yadda zai ci gaba da makure jam’iyyar PDP. Atiku ya sake tafka kuskuren ficewar daga PDP, maimakon tsayawa ya ga ya kwato ta daga hannun Wike da APC. Sannan ya koma ya kwanta tsawon kusa da shekaru biyu ba tare da wata jam’iyya ba. A karshe ya dauko ADC.
Cikin shekarar da ta gabata, na yi kokarin jawo hankalin Atiku game da barcin da ya ke yi domin ya farka ya san cewa akwai damar ADC ta yi tasiri, musamman idan muka yi la’akari da tsarin tattalin arzikin kasa na jam’iyya mai mulki, musamman yadda ya ke ta tatse talaka Yana azurta tsirarun yan siyasa masu mulki. Amma kiran nawa bai sami shiga ba, domin Atiku ya ci gaba da harkokin sa tamkar basaraken gargajiya ba dan siyasa ba, wato maimakon zakulo masu basira da kafa think-tank na samun sabbin hanyoyin da zai iya cin zabe, ya gwammace karbar baki a fadarsa da ziyarce-ziyarcen gaisuwar mutuwa ko daurin aure. ADC na tsammani saboda talaka ya gaji da APC shikenan suna kwance ba tare da aiki tukuru ba wajen kamfe da bijiro da sabbin hanyoyin Jan hankalin masu kuri’a, zasu iya karbe gwamnati da sunaye sannanu kawai?
A yanzu daga Atikun sai Obi, Kwankwaso da Amaechi su ka rage, domin El Rufai tuni ya fada tarkon da ya ginawa kansa. Sannan wasu yan siyasa na kudu na cewa dole a baiwa Amaechi takara, baya ga kiraye-kirayen Obasanjo na a hada Obi da Kwankwaso.
A gaskiya Atiku da yan adawa sun makara, domin APC na da gwamnati, da kudade da kuma mutane masu matukar basira ta yaudara. Sannan sun riga sun kassara adawa gaba daya, sun janye gwamnoni da yan majalisa, sarakuna, malamai da duk masu fada a ji. Kuma zasu iya raba taliya da shinkafa ga talaka. Idan ba wani kadaru na Allah ba, ban ga ta inda za’a kayar da Tinubu a 2027 ba. Kuma la’akari da yadda Arewa ta kasance a tsakanin 2023-2026, Arewa zata shiga mummunan halin da ba a zato daga 2027 abinda ya yi gaba.
Shin Atiku ne kadai ya yi gyangyadi a zaben 2023, amma ya zarce da minshari a yayin da aka doshi zaben 2027, ko har da mu Yan Najeriya?
Malam Ali manazarci ne mazaunin Kano
