Ai Arewa ta tsallake siraɗin Orkar

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

In ba ‘yan lakada-kawas ba da kuma ba mamaki wadanda ba su tashi a gaban dattawan kwarai ba, duk masu nazarin lamuran Arewa ba za su manta da yunkurin juyin mulkin 22 ga Afrilu 1990 ba da Manjo Gideon Gwaza Orkar ya jagoranta kuma ya yi wuf ya kori jihohin kokuwar Arewa daga Nijeriya. Duk muradunsa na dangantaka da yaƙi da tauhidi da kuma bunƙasa kantar ƙabilanci. Tabbas waɗannan muradun na Gideon Gwaza Orkar su ka kifar da yunƙurin kuma ya bar Arewa daram kamar yadda masu jajayen kunne su ka jarraba su ka yi bugun duniya amma a banza tamkar mai neman sare bishiyar kuka da almakashi. Shin akwai ribar faɗawa maliya da yasa? Ido ai mudu ne amma ba na gero ba.

Attajiri Great Ogboru a ka samu da hannu dumu-dumu wajen ɗaukar nauyin yunƙurin. Orkar ya na Dan Arewa kuma makwabcin Janar Babangida amma bai yi nazari ba ya biyewa su Kanar Anthony Nyiam, Manjo Saliba Mukoro da Manjo Cyril Obahor don kifar da gwamnati da watsar da Arewa daga ƙasar ORKANIZATION/MIDIBILIZATION,

Idan mai jan kunne ya buga ya kasa buge Arewa. Idan mai kakin soja da igwa ya harba amma barushi ya juyo ya gama da shi; ina ga Bazatawa na karshen zamani za su iya. Shawara su saduba kawai don tabbas hanyar nan ba za ta ɓulle ba.

Wallahi ba wayonmu ba ne kuma ba dabararmu ba ce, taimakon mahaliccin sammai da kassai ne wanda ke yin yadda ya so a lokacin da ya so ko da Bazatawa ba sa so. Don haka ina kira ga dukkan ‘yan uwa da dagewa a ‘yan sauran kwanakin nan na watan nan na Ramadana mai albarka, mu kara godewa Allah kan kariyar da ya ke yi ma na da tsare Lardinmu mai albarka. Allah ya sa in mun gode ma sa zai ƙara ma na alherinsa marar iyaka.

Haƙiƙa burin maƙiya ya ƙasa cika don haka su ke kwaso dukkan makamansu don a yi gumurzun karshe. Arewa fa ta zama a daka, a kada a rawa sai kalwa. 

Duk mai bin tarihi in ba matasa da ‘yan lakada-kawas na ‘yan bazatan zamanin soshiyal midiya ba, ya san waya ce Hajiya Maryam Babangida mai BETTER LIFE FOR RURAL WOMEN. An haife ta a 1948 a Asaba jihar Delta. Sunanta na asali Maria Ndidi Okogwu kuma ta karɓi Musulunci a lokacin aurensu da Janar Babangida da ya gudana a 1969 kuma Allah ya yi ma ta rasuwa bayan fama da jinyar sankara a 2009. Ita ce mahiafiyar Muhammad Babangida da Janar din kansa ke kira MO.

A daren yunƙurin juyin mulkin nan na Manjo Gideon Orkar, shugaban mulkin soja Janar Babangida ya sallami bakinsa na ƙarshe kuma gabanin ya kwanta, ya kunna talabijin ya duba don ganin labarun tsakar dare ko akwai wani sabon abu amma bai ga komai ba. Ikon Allah sai Hajiya Maryam ta zaga bayan gida sai ta leƙa ta taga ta ga sojojin ‘yan bazata na ɗaukar saiti a wajajen da ba sabam ba da hakan ya nuna akwai matsala. Ba ta rikice ta kwarma ihu ba. Nan ta shaidawa Janar halin da a ke ciki, shi ma ya leka ya gani daga nan ya ankarar da jami’an tsaronsa waɗanda tuni sun san abun da ke faruwa. Dogarinsa Laftanar Kanar UK Bello ya shiga aiki na ba da kariya. An ci nasarar kai Janar da mutan gida tudun mun tsira duk da a ra’ayinsa ya zauna a gidan ta fanjama-fanjam.

Janar Babangida ya raina tunanin su Orkar na cusa kabilanci a yunkurin da nuna ƙiyayya ga fadar Sultan da hakan ya kai ga sallamar jihohin Arewa 5 daga Nijeriya. Jihohin 5 a zamanin yau, sun zama 10 domin na farko akwai Bauchi da ta samar da Gombe, akwai Borno da ta samar da Yobe, akwai Kano da ta samar da Jigawa, akwai Katsina da dama a ka ƙirƙiro a 1987 daga Kaduna. Sai Sokoto da ta samar da Zamfara da Kebbi.

Bayan nan UK Bello ya dawo ya tinkari su Gideon Orkar. A nan dai har Orkar ya gargadi Bello da ya janye jajircewa don dama abokinsa ne. Tsayin dakar Bello ya ba wa uban ‘yan bazatan dariya don dama tun wanshekare, sun turo wani injiniyan gyaran makamai ya kunce damarar kunamun kariyar barikin Dodan. UK Bello ya yi wuf ya shiga tankar yaki don fara bude w+ta ashe an wargaza kunamar. Nan su Orkar su ka yi ma sa ruwan sama na albarusai fafaffafaffafa tarakkakat nan su ka yi nasarar kashe shi. Marigayi Janar Sani Abaca da dakarunsa su Manjo Hamza Almustapha su ka tinkari Bazatawa kuma su ka yi nasarar murƙushe yunƙurin.

Har zamanin nan na yau ajandar Orkar ce ‘yan bazata ke yunkurin tabbatar da ita ta kifar da Arewa kowa ma ya huta da jin kiran sallah. Da ka yi magana za su ce tun zamanin Mujaddadi a ka yaudari kakanninsu da addini, wai yanzu sun waye ba za su yarda ba. A nan zan ce ba bukatar yarda ko rashin yarda, m+sulunci ba mallakar Shehu ba ne kuma ba addinin Larabawa ba ne kamar yadda ‘yan kudu ke tunani, addinin Allah ne. Maimakon neman tada fitina, kowa ya yi addininsa cikin girmama juna tun da ba wanda zai iya korar dan uwansa daga kasar. Batun kabilanci kuma ba zai samu karɓuwa ba sam-sam a Musulunci, addinin Allah ba na Shehu ba don Shehu bai taba cewa shi ne Musulunci ba. Kafin a haifi Shehu ma musulunci ya yi fiye da shekara 1168 daga hijira.

Duk mai lura da yadda lamura ke gudana, zai fahimci muradun ‘yan bazata na gefe daya abun da su ke fakewa da shi na kalubalen tsaro na daya gefen. Ina mai tabbatar mu su ko za su shekara 1000 su na wannan kisisina ba za su samu nasara ba, amma ba mamaki su more bakinsu da rubutun da su ke yi na cin zarafin waɗanda su ka tsana da murde wuyan tarihi dare da rana. An yi walkiya.

Shin tsakani da Allah su wa su ka ruga Amurka su ka kai ƙorafin a na kisan kare dangi na addini a Arewacin Nijeriya? Ai kowa ma ya san amsar. To Amurka ta shigo Nijeriya har ma watannin baya ta kai farmaki yankin Sokoto kuma ta yi bayani ta samu nasara kan ‘yan ta’adda. ‘Yan bazata sun yi ta tsalle su na murna su na godiya ga shugaba jan-kunne mai hana-sallah da ma dan lelensa mai buga kugen yaƙi har ma da yin zane-zane na ATRFICIAL INTELLIGENCE su na iƙirarin wani Shehun malami na arcewa don neman maboya. Bazatawa sun dauka za a kai farmaki kan kujerar jikokin Shehu Mujaddadi waɗanda ke wakiltar miliyoyin al’ummar tauhidi. Sai tsit ka ke ji don Allah maɗaukakin sarki ya kiyaye yankin Arewa da ya sha albarka daga Mujaddadi. Mun yi imani in wani abu kyakkyawa ko mummuna ya zo ma na na jarrabawa sai mu miƙa lamarinmu ga Allah.

Waɗanda su ka raina kokarin zaratan jami’an tsaron Nijeriya su ka garzaya Amurka don ta shigo Nijeriya ta dau matakan a yi ta-ta kare, kan manta cewa Najeriya kasa ce mai ‘yanci kuma haka kawai Amurka ba za ta jefo makamai masu linzami kan jama’a da ba su da laifi ba don zangar wasu na zaginsu da shafa mu su bakin fenti dare da rana a soshiyal midiya. Kazalika dakarun na Amurka sun bayyana za su yi aiki ne da sojojin Nijeriya. Su fa Bazatawa sun dauka Amurka za ta riƙa tambayarsu ina ya dace a kai wa hari, wa ya dace a murƙushe da sauran su. Kai na ga wani ɗan bazata ma na nuna taswirar zolaya wai ya dace shugaban Amurka ya fahimci banbancin Bauchi da Auchi don kar garin kai farmaki Bauchi makami ya yi batan kai zuwa Auchi. Haka ma wani ya rubuta shugaban ya tantance bambancin Katsina ta jiha da Katsina-Ala ta karamar hukuma a jihar Binuwai. Ga su nan dai mutane masu mugun nufi don kantar da kiyayya ta yi a zuciyarsu.

KAMMALAWA

Mutanen nan na nuna tamkar shigowar Amurka aikin baban-giwa ne don wai kamar hare-hare ƙaruwa su ka yi. Hanya mafi inganci ga duk ‘yan kasa ita ce marawa gwamnati baya da daina raina jami’an tsaron kasa musamman ta miyagun rubuce-rubuce a yanar gizo. Ba wata kasa a duniya da za ta yi ma na tasirin da mu kanmu da gwamnatinmu za mu yi wa kanmu. Zagin jami’an gwamnati da furta kalmomi na ƙabilanci da tsamar bambancin addini ba zai kawo maslaha ba sam. Duk da haka na san su Bazatawa ba sa son fitinar ta tsaya don ta nan ne burinsu na wargaza Arewa zai cika, amma yadda su ke son a wulaƙanta wasu ne da su ka tsana kuma sun ga hakan ba mai yiwuwa ba ne, shi ya sa yanzu su ka juyo su na neman kushe amsar madugun jan kunne na farar faɗa. Ba mu da zaɓi da ya wuce marawa fadar dutse baya a lamarin tsaro don ba abun da zai yi nasara hatta damar baje kolin ƙabilanci da bambancin addini sai da zaman lafiya a birane da karkara.

By ukarofi