Yadda Gwamna Uba Sani ya biya diyya ga waɗanda El-Rufai ya yi wa rusau

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta fara cika alƙawarin da ta ɗauka na tabbatar da adalci ga al’ummar unguwar Malali Low-Cost, inda ta miƙa sabbin filaye ga mazauna yankin da aka rushe musu gidaje a zamanin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Bayanai da Tsarin Filaye ta Jihar Kaduna (KADGIS), Dakta Bashir Garba Ibrahim, ne ya jagoranci rabon takardun mallakar filayen ga waɗanda abin ya shafa.

Ya bayyana cewa, wannan mataki wani ɓangare ne na cika alƙawarin da Gwamna Uba Sani ya yi na ganin an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.

Dakta Bashir Ibrahim ya ƙara da cewa, rabon filayen ya samo asali ne daga taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar 21 ga Janairu, wanda ya mayar da hankali kan binciken yadda aka gudanar da rusau a lokacin gwamnatin da ta gabata.

Yayin da yake miƙa takardun filayen, ya shawarci waɗanda suka amfana da su da su gaggauta gina gidaje a wuraren, tare da gargadin su da kada su sayar da filayen.

A cewarsa, gwamnati na son ganin sun zama masu gidaje na dindindin kuma su ba da gudunmawa ga ci gaban jihar.

Da yake jawabi a madadin waɗanda abin ya shafa, shugaban tsofaffin mazauna Malali Low-Cost, Alhaji Mohammed Auwal, ya gode wa Gwamna Uba Sani bisa wannan mataki, yana mai cewa hakan ya kawo ƙarshen wahalhalun da suka shafe kusan shekaru tara suna fama da su wajen neman diyya.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin Babban Daraktan KADGIS wajen ganin an samu wannan nasara, yayin da sauran mazauna yankin suka bayyana gwamnatin a matsayin mai tausayi da kulawa ga al’umma.

Tarihi ya nuna cewa a watan Oktoban 2020, Kamfanin Raya Kadarori na Jihar Kaduna (KSDPC) ya bai wa mazauna Malali Low-Cost wa’adin kwana bakwai su bar gidajensu.

Wannan mataki ya haifar da zanga-zanga daga mazauna yankin, wanda ya sa aka dakatar da shirin a wancan lokaci.

Sai dai a watan Maris na 2021, an sake ba su wa’adin kwana uku, inda bayan ƙarewar lokacin aka rushe sama da gine-gine 80 a matakin farko. 

Tun daga lokacin ne waɗanda abin ya shafa suka ci gaba da neman diyya ko kuma madadin filaye daga gwamnati, kafin wannan sabon mataki ya kawo sauƙi ga damuwarsu.

By ukarofi