Daga USMAN KAROFI
Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon fashewar bam da ya rutsa da wata motar haya kusa da ƙauyen Woro, a ƙaramar hukumar Kaiama, Jihar Kwara. Wannan lamari ya faru da safiyar Litinin, 23 ga Maris 2026, da misalin ƙarfe 7:43 na safe, lokacin da motar ke tafe daga ƙauyen Wurumakoto zuwa New Bussa a Jihar Neja.
Direban motar, Malam Zubairu, ya yi tafiya ba tare da sani ba a kan bama-bamai da aka saka, wanda suka fashe nan take a kan motar. Fashewar ta kashe direban nan take, sannan ta jikkata wasu fasinjoji sosai, yayin da ake fargabar wasu sun rasa rayukansu. Waɗanda suka jikkata an garzaya da su asibiti na New Bussa don samun kulawar gaggawa.
Hukumomin tsaro sun yi zargin cewa bama-baman sun kasance na wasu ƙungiyoyin tada ƙayar baya da ke aiki a yankin, waɗanda ake zargin su ne suka yi irin wannan hari a yankin Woro a watan da ya gabata. Sojoji da jami’an tsaro sun tura jami’ai zuwa wurin don gudanar da ayyukan tsabtace yankin, inda aka gano wasu bama-bamai kuma aka warware su lafiya ta hannun ƙwararru daga sansanin soja na Kaiama.
Duk da ƙarin jami’an tsaro a yankin Kaiama–Woro, wasu ‘yan ta’adda sun canza dabarun su ta hanyar amfani da bama-bamai na hannu. Har ila yau, ƙauyen Woro da kewaye sun sha fama da tsananin rashin tsaro a ‘yan makonnin baya, bayan wani harin da ya kashe mutane da dama tare da sace wasu a watan Fabrairu.
