Ayyukan raya ƙasar Bichi sai a Abuja ko ƙasashen ƙetare – Ahmad Bichi

Spread the love

A cigaba da wanzuwar ayyukan raya ƙasa da gina rayuwar jama’a da ɗan majalisar tarayya, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar ke ta gudanarwa, jami’ar yaɗa labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta samu zanta wa da wasu daga cikin injiniyoyi da manajojin ayyukan raya ƙasa na gani da ido hannu ya taɓa, sakamakon katafariyar katangar da ɗan majalisar ya ɗauki salon zagaye gine-ginen manyan ma’aikatu da hukumomin yankin domin jin daɗi da walwalar jama’a da kuma tsaro.

Arc Imam Mukthar Sa’ad, ya tabbatar da aikin tun da aka fara shi ba a tsaya ba, komai yana tafiya yadda ya kamata ƙarƙashin sahalewa da umarnin ɗan majalisar, kazalika sabuwar katangar kuma, rukunin da za ta zagaye sun haɗa da; sakatariya da sauran.

Domin a cewarsa, ‘haƙiƙa wajen zai ƙara zama alƙarya bisa kyakkyawan fasalin da zai bayyana a babban titin, da zarar an kammala aikin nan gaba kaɗan ba tare da ɗaukar lokaci mai tsawo ba.’

“Watan da ya gabata muka fara aikin, kuma in sha Allahu nan da wata ɗaya zuwa biyu muna sa ran kammalawa baki ɗaya.” Imam Mukhtar Sa’ad Bichi.

A jawabin Ahmad Umar da ke Mazaɓar Bichi, ya ce, irin yadda aka tsara ginin katangar da ƙarko da tsawo, babu shakka yana da alaƙa da alkinta dukiyar gwamnati da al’umma, tare da cigaba ta hanyar bunƙasar ƙaramar hukumar mai ɗorewa.

“Gaskiya ɗan majalisar tarayya yana kawo ayyukan cigaba sosai, waɗanda ba yanzu ma za a ga amfaninsu ba sai nan gaba kaɗan, ayyuka ne irin waɗanda ba a samunsu a ƙananan hukumomi sai ka je manyan birane; irinsu Legas, Abuja da ƙasashen ƙetare!” Ahmad Umar Bichi

By ukarofi

Leave a Reply