An yi kira ga gwamnatin Katsina ta haramta bukukuwan kammala sakandire da ɗalibai ke yi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta haramta gudanar da bukukkuwan graduation party da sign out a dukkan makarantun sakandare da manyan makarantu da ke faɗin jihar.

A zaman majalisar na ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Rt. Hon. Abduljalal Haruna Runka, bayan ƙudurin da Hon. Aliyu Abubakar Albaba, mai wakiltar Katsina, ya gabatar. Ya ce hakan zai taimaka wajen mayar da hankali kan ilimi da tarbiyyar ɗalibai.

Hakazalika, majalisar ta buƙaci gwamnatin jihar ta gaggauta gyaran hanyar Fanga zuwa Kafin Dangi zuwa Bindawa ta miƙe zuwa Agalawa ta je Yar Liman har Zakata zuwa Jani, wadda ta ratsa ƙananan hukumomin Bindawa, Kankia da Mani.

Ƙudurin ya fito ne daga Hon. Umar Ali Bindawa, wanda ya bayyana muhimmancin hanyar ga zirga-zirga, kasuwanci da rayuwar al’umma.

A zaman, babban mai binciken kuɗaɗen ƙananan hukumomi na Jihar Katsina, Alhaji Sha’aibu Aliyu, ya kuma gabatar da rahoton binciken kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar na shekarar da ta ƙare a ranar 31 ga Disamba, 2025.

Bayan tattaunawa kan ƙudurorin, mataimakin kakakin majalisar ya umarci akawun majalisar da ya tura su ga ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi

Leave a Reply