Jami’ai takwas sun rasu bayan motocin sojoji sun bi ta kan bom a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla sojojin Nijeriya takwas ne suka rasu bayan tawagar motocinsu ta bi ta kan wani abin fashewa da aka zargi mayaƙan ƙungiyar ISWAP da dasawa a Jihar Borno.

An gano cewa, al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da dakarun Birget na 24 na Task Force a Dikwa suke koma wa sansaninsu daga Maiduguri bayan rakiyar wasu motoci da suka yi dakon kayan abinci da wasu ababe.

A cewar majiyoyin sojoji kamar yadda ShaharaReporters ta ruwaito, motar yaƙi ce ke jagorantar sauran motocin a lokacin da iftila’in ya auku akan hanyar.

Ta ce, baki ɗaya sojojin da ke cikin motar sun rasu a nan take bayan ta taka bom ɗin da aka binnen.

Saidai, ba a tabbatar da sunayen jami’an ba a hukumance yayin haɗa wannan rahoto, amma ana sa ran rundunar sojin ta fitar nan ba da jimawa ba.

Wannan hari ya ƙara adadin farawa irinsa akan manyan titina da ‘yan ta’adda ke amfani da shi wajen farmakar sojoji a shiyyar Arewa maso Gabas.

A watan Yuni ne sojoji uku suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan motar sojoji ta taka bom akan titin Marte zuwa Dikwa, wato babbar hanyar da sojoji ke amfani da ita wajen zirga-zirga a Jihar Borno.

Haka ma a 2025, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi wa tawagar motocin sojoji kwanton-ɓauna a yankin Dikwa, lamarin da ya yi ajalin soja huɗu da lalata manyan motocinsu guda biyu.

Masu sharhi na alaƙanta ƙarin hare-haren a matsayin wani samun wani salo daga ɓangaren mayaƙan wajen dogara da dasa bom a gefe ko kan hanya a madadin fuskantar dakarun tsaron gaba-da-gaba.

Mafi yawancin boma-boman ana dasa su ne a hanyoyin da aka san sojojin na amfani da su wajen zirga-zirgar jami’ai, safarar kayan abinci, fetur da wasu ababen amfaninsu a tsakanin Maiduguri, Dikwa, Bama da ƙananan hukumomi mafi kusa da su.

By Babaji

Leave a Reply