Ba a bayyana nasarorin Tinubu yadda yakamata – APC

Spread the love

Tony Okocha, Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar APC a jihar Ribas, a ranar Lahadi a Abuja, ya ce nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya samu ba a bayar da cikakken rahotonsu yadda yakamata.

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron tattaunawa na kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), yana mai cewa akwai buƙatar ministocinsa su ƙara wayar da kan ‘yan Nijeriya game da nasarorin wannan gwamnati.

“Nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu ba sa bayyana ga jama’a saboda mafi yawan ministocinsa sun kasa yin abin da ya kamata kuma ba su ƙara wa gwamnatin daraja.

Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, gwamnatin Tinubu ba ta yi mummunan aiki ba, musamman idan aka yi la’akari da irin mawuyacin halin da ta gada.

Mista Okocha ya ce yayin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta yi aiki sosai ba, gwamnatin yanzu na aiki dare da rana don sake farfaɗo da ƙasa.

Ya ce abin takaici ne yadda yawancin ministocin gwamnatin Tinubu ba a san su ba saboda ba su da tasiri kuma ba su da wata hanya ta yaɗa nasarorin gwamnati da ayyukanta.

“Nasarorin da shugaban ya samu cikin ƙasa da shekaru biyu ba sa bayyana, har sai ya yi jawabi, za ka san me a kayi.

“Dole ne wani ya ɗauki nauyin sanar da ‘yan Nijeriya abin da gwamnati ke yi a cikin ma’aikatun, kuma duk waɗannan abubuwan da aka tara su ne nasarorin shugaban kasa,” in ji Mista Okocha.

By ukarofi