Kwamitin raba biliyan ɗaya da Bafarawa ya bayar: An ɗora ƙwarya a gurbinta

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Kyakywan tsari da zai iya haifar da ɗa mai ido ne aka shirya don ganin kaso mai ɗan nauyi na mabuƙatan da ke cikin Jihar Sakkwato sun mora daga kuɗaɗen da tsohon gwamnar Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru ɗalhatu Baffarawa ya bayar don rage raɗaɗi ga halin matsin rayuwa da ake ciki.

Shirin wanda zai bada damar ba wa kowacce ƙamar hukuma da ke da mazauni a jihar, daga ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin Sakkwato, damar samun kaso na daga ayyuka ko tallafi daga kuɗaɗen, shiri ne da ya zo da tsari irin tsarin da za mu iya cewa, ire-irensa na farko da ake gudanarwa yayin bayar da tallafi.

Koda yake bai zama abin mamaki ba, lakari da wanda ke jagoranatar raba kuɗin, wato Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato ba, duba da jajircewa tare da riƙon gaskiya yayin gudanar da ayyukan amana, da tabbatar da inda ake buƙatar abu ya isa ya kai ba tare da matsala ba.

A ranar Talatar da ta gabata ne, aka gudanar da zama na musamman ƙarƙashin jagorancin Injiniya Muhammad Lawal, wanda ya haɗa wakilai huɗu daga kowacce ƙaramar hukuma da ke faɗin jihar.

Wannan kuwa wani yunƙuri ne na ganin an samar da daidaituwa yayin da ake raba wannan tallafin.

Kwamitin wanda babban kwamitin da shi Injiniya Lawal ke shugabanta ya kafa, a ƙoƙarin samar da mabambantan shawarwari kan yadda za a tafiyar da rabon kuɗaɗen ga al’ummar Sakkwato, ya yi zamansa ne a gidan uban gayya kuma silar haɗuwar, wato Garkuwan Sakkwato, kuma tsohon gwamnan jihar.

Tun daga farko, shugaban taron, Sadaukin Sakkwato, ya fara da jawabi mai tsayi ga mahalarta, wanda daga ciki ya yi jan hankali tare da kira ga zaɓaɓɓun wakilan ƙananan hukumomin da su zama wakilai na gari, su tsayar da gaskiya tare da cire son rai yayin zaɓen waɗanda suke buƙatar tallafin.

Maidoki, ya kuma ƙara da bayyana guraben da tallafin zai shafa, da kuma yadda ake so wakilan su gudanar da aikin.

Daga cikin ababen da za a fi mayar da hankali, akwai harkar ilimi, wanda aka ba wa kowacce ƙaramar hukuma damar zaƙulo mutane goma (wanda aka fi son a daidaita tsakanin maza da mata idan hakan zai samu), na daga yaran da suka kammala babbar sakandare, don ba su damar yin jarrabawa ta musamman da za ta kai su ga cin damar yin karatu kyauta daga kwasa-kwasan da suka shafi harkar laliya.

Wannan damar kuwa an yi mata shiri tsaf, ta hanyar tanadar fom da yaran za su cika ƙarƙashin jagorancin wakilansu na ƙananan hukumomi, da kuma gabatar da takardun karatun su.

Wani abin birgewa na wannan tsari kuwa shi ne, yadda aka sawwaƙa wa yaran zuwa jarrabawar ta alƙawarin bayar da kuɗin mota ga duk wani ɗalibi da aka gayyata.

Baya ga goyon baya da suka samu daga wasu makarantu na karatun aikin lafiya, kamar wadatattun guraben karatu, kai har ma da ba su gudunmuwa ta hanyar zabtare wani kaso na kuɗaɗen da za a kashe na ɗawainiyar wannan karatu.

Duk wannan shirin zai kasance a ƙarƙashin kulawar ƙwararrun da suka jima suna bayar da gudunmuwa a harkar ilimin ‘ya’ya mata musamman a karkara, wato NANA Girls and Women Empowerment Initiatiɓe, waɗanda za a miƙa ragamar biyan karatun yaran da suka ci jarrabawa daga farko har ƙarshe a hannunsu, inda za a miƙa adadin da lissafin ya bayar ciki kuwa har da kuɗin zuwa makaranta ga kowane ɗalibi har ya kamala.

Ba a iya nan za a tsaya ba, Sadauki, ya kuma yi ƙarin bayani kan ɓangaren ba wa ciki tallafi, inda ya ce, za a ware buhu ɗari ga kowacce ƙaramar hukuma, da za a siya daga kuɗin don raba wa jama’a, wanda su wakilan za su zaƙulo waɗanda suka dace a ba wa, tare da kuɗin jar miya kimanin dubu goma ga kowane buhu guda.

Ya kuma yi ƙarin haske kan yadda kowacce ƙaramar hukuma ta ke da damar zaɓar nau’in abincin da take so a raba mata, wato daga shinkafa, gero, garin kwaki da sauransu.

Sannan kuma, an ware wani kaso ga ‘yan gudun hijira, waɗanda a halin yanzu suka fi yawaita a ƙananan hukumomi biyu, kuma ya tabbatar da an yi zama don jin abinda suka fi buƙata, kuma sun zaɓi garin kwaki a matsayin muradinsu na daga abinda za a ba su na tallafin.

Har wa yau dai, a cikin kuɗaɗen za a waiwayi sha’anin lafiya, wadda aka ce uwar jiki, inda aka ba wa wakilan aikin zaƙulo waɗanda ke da lalurar da ke buƙatar aiki, kuma babu abin yin aikin, don biya musu kuɗaɗen, a ƙoƙarin samar masu da lafiya, kuma su amfana daga wannan tallafin.

A ɓangaren ruwa kuwa, wakilan a ƙarƙashin amincewar kwamitin zartarwa, za su zagaya ciki da bai na ƙaramar hukumarsu, don samo wuraren da ke fama da matsalar ƙarancin ruwa, masu buƙatar rijiya, ya Allah sabuwa ce, ko kuma wadda ta lalace take buƙatar gyara, don ba su damar mora daga cikin abinda tsohon gwamanan ya bayar.

Daga ƙarshe an ba wa wakilan damar bayar da ta su shawarwari, kuma an tattauna kan waɗanda aka bayar tare da buɗe ƙofa ga waɗanda ke son ƙara bayarwa ta hanyar bayarwa a rubuce, duba da lokaci da kuma nisan inda wasu suka fito.

Tun daga yananyin tsarin, da kuma jajircewa da na hango a tattare da wakilan har ma da shugabanni a wannan taro, zan iya cewa, tabbas an ɗora ƙwarya a gurbinta, don haka Sakkwatawa, ku sha kuruminku, domin ba tare da wahala ko sanin wani ba, tallafin zai isa ga mai rabo da yardarm Allah.

Taro ya waste bayan an gabatar da abinci ga dukkan mahalarta da kuma kuɗin mota daidai da nisan inda ka fito.

Asas ce Editar Mata da Al’adu ta Blueprint Manhaja da ake wallafawa a Abuja

By ukarofi