Yadda ƴan kasuwa suka shigo da fetur lita miliyan 123 don rage nauyi ga Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Aƙalla gungun maɗaukai huɗu ne ɗauke da man fetur suka iso tashoshin jiragen ruwan Nijeriya daga ranar 18 zuwa 20 ga watan Oktoba.

Cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen ruwa (NPA) ta fitar, ta ce aƙalla man da aka yi dakon su zuwa ƙasar sun kai kusan lita miliyan 123.4 don faɗaɗa harkar raba fetur a Nijeriya.

Rahotonni sun bayyana cewa, dilolin sun yi hakan ne don rage nauyin samar da fetur ga matatar Ɗangote, inda suka ce adadin da ta ke samarwa ya yi kaɗan ga duka sassan Nijeriya.

Sun yi zargin cewa matatar ta Ɗangote ta na samar da lita miliyan 10 ne kaɗai a kowacce rana a madadin lita miliyan 25 da ta yi alƙawari da farko.

A watan Satumba ne ƴan kasuwan suka shigo da kusan lita miliyan 141 bayan samun hauhawar farashin fetur da aka yi daga wanda matatar Ɗangoten ta samar, wanda kuma Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL ya fitar da shi.

Wannan mataki da ƴan kasuwan suka ɗauka ya faru ne sakamakon dama da suka samu daga gwamnati da hukumar tace ɗanyen man fetur ta ƙasa ƙarƙashin dokar ƙayyade farashin fetur.

By Babaji