Daga USMAN KAROFI
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bayyana cewa babu wani muƙaddashin babban hafsan sojojin Ƙasa (COAS) da aka naɗa, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa. A cewar wata sanarwa da ta fitar, an bayyana cewa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja yana kan hutun shekara, kuma babu wani sabon naɗe-naɗe a cikin rundunar.
Sanarwar ta kara da cewa dukkan hafsoshin soji suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Manjo Janar Abdulsalami Bagudu Ibrahim, wanda yake babban hafsan tsare-tsare da shirye-shirye na sojojin ƙasa, yana ba da rahotanni na yau da kullum ga babban hafsan sojojin ƙasa, yayin da Lagbaja ke kan hutun.
An yi bayanin cewa wannan mataki yana daga cikin tsare-tsare na soja da aka saba aiwatarwa, kuma babu wani gibi ko rashin shugabanci a rundunar soji.
Hedikwatar Tsaro ta yi kira ga duk wanda ke yaɗa jita-jitar cewa an naɗa muƙaddashin COAS da su daina wannan aiki na yaɗa labaran ƙarya. Ta yi nuni da cewa Babban Hafsan sojojin ƙasa yana cikin ƙoshin lafiya kuma zai dawo bakin aiki nan ba da jimawa ba bayan ya kammala hutun sa.
Haka kuma, DHQ ta yi gargaɗi kan wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda wasu ke kira da a yi juyin mulki. An bayyana irin wannan kira a matsayin cin amanar kasa wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, kuma hakan laifi ne mai tsanani. Rundunar sojojin Nijeriya ta jaddada aniyar ta wajen tabbatar da dimokuraɗiyya a Nijeriya, tare da cewar tana nan daram wajen kare mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma martabar ƙasar.
