Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Raɗɗa, ya jaddada matsayar gwamnatinsa na ƙin tattaunawa da ‘yan bindiga, sai dai gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina za ta yi maraba da duk wani shirin zaman lafiya da nufin magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.
“Mutane da yawa a jihar Katsina suna maganar cewa ana yin sulhu da ‘yan ta’adda, mu kuma muna gaya wa mutane cewa ba gwamnatin jihar Katsina ke yin sulhu da ‘yan ta’adda ba al’umma dake wuraren da abun ya shafa ke yin sulhu da su, mu duk wanda ya amince a yi zaman lafiya mu ma zaman lafiyar muke nema,” inji shi.
Raɗɗa, ya bayyana hakan a ranar Laraba wajen bikin yaye jami’an tsaron jihar, wato Katsina Community Watch Corps (CWC), kashi na uku, gwamnan ya nanata cewa al’umomin jihar ne ke tattaunawa da ‘yan bindigar a sassan jihar, ba wai shirin gwamnati ba ne.
Sai dai gwamnan ya ce duk inda aka yi irin wannnan zama na sulhu ana samun zaman lafiya, saboda haka ne ya yi alƙawarin bada gudummuwa don zaman sulhun ya ɗore.
Gwamnan, ya ce tsarin shiri ne mai cikakken tsari wanda ke ba wa al’ummomin da abin ya shafa damar ƙulla yarjejeniya da tubabbin ‘yan bindiga waɗanda suka amince su ajiye makamansu.
