Nnamdi Kanu na da lafiyar fuskantar shari’a – Likitoci ga kotu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tawagar ƙwararrun Likitoci a Nijeriya (NMA) ƙarƙashin jagoranci shugaban ƙungiyar Likitocin ƙasar, sun tabbatar da cewa rashin lafiyar da aka ce na damun shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafira ta IPOB, Nnamdi Kanu ba wata babbar damuwa ba ce.

Mai shari’a James Omotosho ne ya umarci tawagar likitocin ta duba lafiyar Kanu, bayan da lauyoyinsa suka yi iƙirarin cewa yana fama da wata jinya.

Cikin rahoton binciken tawagar ƙwararrun likitocin, da aka miƙa wa kotu ranar 13 ga watan Oktoban da muke ciki, ya ce rashin lafiyar da ke damun Kanu ba mai barazana ba ce.

Tawagar likitocin ta ce bayan auna lafiyar Kanu sun tabbatar da cewa za a iya ci gaba da yi masa shari’a, domin kuwa zai iya halartar kotu.

Bayan karɓar rahoton, Mai shari’a Omotosho ya ce kotun ta gamsu da rahoton don haka za a ci gaba da shari’ar.

Da yake dogaro da sakamakon kwamitin kuma ba tare da wata hamayya daga kowane ɓangare ba, Mai shari’a Omotosho ya yanke hukuncin cewa a ci gaba da shari’ar sannan ya baiwa wanda ake ƙara kwanaki shida a jere, daga ranar 23 ga Oktoba, ya buɗe tare da rufe kariyarsa.

Alƙalin ya kuma amince da buƙatar da babban lauyan Kanu, Kanu Agabi (SAN), ya gabatar na tattaunawa ta sirri tsakanin wanda ake ƙara da tawagarsa a wajen hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), inda ya nuna damuwa kan yiwuwar sa ido.

Mai shari’a Omotosho ya bayar da umarnin a gudanar da ganawar sirri a cikin kotun daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 12:00 na rana ranar 22 ga watan Oktoba, gabanin ci gaba da shari’ar.

By ukarofi