Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa ta diflomasiyya da gwamnatin Amurka kan sabon zargin wasu ‘yan majalisar dokokin ƙasar cewa Nijeriya na da hannu wajen cin zarafi da kisan gillar da ake yi wa Kiristoci.
An ruwaito cewa ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta tabbatar da cewa ta tuntuɓi gwamnatin Amurka ta ofisoshinta na jakadanci a biranen Washington da Atlanta, tana musanta abin da ta kira “zarge-zarge marasa tushe da suka cike da ruɗani” da wasu ‘yan majalisar Amurka ke yaɗawa.
Rigimar ta samo asali ne daga ranar 11 ga Satumba, lokacin da Sanata Ted Cruz daga jihar Teɗas ya gabatar da ƙudirin doka a majalisar dattawan Amurka mai suna Nigeria Religious Freedom Accountability Act of 2025 (S.2747).
ƙudirin na neman a mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake wa kallon masu take hakkin addini (“Country of Particular Concern” – CPC), wanda hakan zai iya jawo wa ƙasar takunkumin diflomasiyya da tattalin arziki.
Nijeriya dai ta fara shiga wannan jerin ne a watan Disamba 2020 a lokacin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, kafin gwamnatin Joe Biden ta cire ta a Nuwamba 2021, inda ta ce ba ta ga hujjar da ke nuna gwamnatin Nijeriya tana da hannu kai tsaye wajen cin zarafin ‘yancin addini ba.
A cikin sabon ƙudirin, Sanata Cruz ya zargi gwamnatin Nijeriya da yin shiru ko tallafa wa “cin zarafi da gallazawa” da ake yi wa Kiristoci da ‘yan tsiraru na addini ta hannun Boko Haram da wasu ƙungiyoyin makiyaya. Ya kuma nemi a sanya wa jami’an Nijeriya takunkumi ta hanyar hana biza, toshe asusu, da kuma dakatar da tallafin Amurka har sai an nuna bin doka.
Bayan hakan, wasu Sanatoci biyar na jam’iyyar Republican, ƙarƙashin jagorancin Sanata Ted Budd, suka aike da wasiƙa ga sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, suna kira da a gaggauta maido da Nijeriya cikin jerin CPC.
Sun ce sama da Kiristoci 52,000 aka kashe tun daga shekarar 2009, kuma an lalata majami’u da cibiyoyin Kirista fiye da 20,000 a faɗin ƙasar.
A cewar rahoton, “a cikin shekarar 2025 kaɗai, mutum 3,100 daga cikin kisan addini 4,476 da aka yi a duniya sun faru ne a Nijeriya,” bisa bayanan da ƙungiyar Open Doors World Watch List ta bayar, wadda ta ce Nijeriya ita ce “ƙasar da ta fi haɗari ga Kiristoci” a duniya.
Har ila yau, wani ɗan majalisar wakilai a Amurka, Riley Moore, ya rubuta wasiƙa ga sakataren harkokin wajen, yana kiran Nijeriya “mummunan wuri ga Kirista,” tare da zargin gwamnati da “rashin aiki da cin hanci.”
Sanata Jim Risch daga Idaho, wanda ke shugabantar kwamitin harkokin waje na majalisar dattawan Amurka, shi ma ya wallafa a shafinsa na ɗ cewa “addini bai kamata ya zama hukuncin kisa ba,” yana mai bayyana halin da ake ciki a Nijeriya da wasu sassan Afirka a matsayin “abin takaici.”
Sai dai duk da matsin lambar da ke tasowa daga ‘yan majalisar Amurka, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan ƙudirin ko kan buƙatar sake sanya Nijeriya cikin CPC ba.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar da cewa gwamnati ta riga ta fara matakan diflomasiyya don mayar da martani da kuma fayyace haƙiƙanin halin da ake ciki.
