Majalisar Dattawa ta amince da Farfesa Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), inda zai maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci hukumar na tsawon shekaru goma.

Rahoton NAN ya bayyana cewa majalisar ta amince da naɗin Amupitan a zamanta, bayan dogon lokaci na tantancewa da ‘yan majalisa suka gudanar.

Farfesa Amupitan, ɗan asalin Jihar Kogi kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos, ya sha alwashin yin aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki kamar Hukumar Katin Shaidar ɗan ƙasa ta NIMC da NCC domin inganta tsarin gudanar da zaɓe a ƙasar.

A yayin amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar, Amupitan ya bayyana cewa, “Ban jagoranci ƙungiyar lauyoyi ta Shugaba Bola Tinubu a kotun ƙara kan zaɓen shugaban ƙasa ba. Ban bayyana a kotun ɗaukaka ƙara ko a Kotun ƙoli ba.”

Haka ɗalika, ya kuma ce zai gudanar da bincike na ciki (audit) a tsarin INEC, musamman kan kayan aiki da hanyoyin gudanar da zaɓɓe, domin gano matsaloli da samar da ingantattun hanyoyi na warware su.

“Ba INEC kaɗai ke da alhakin gudanar da zaɓe ba. Dole ne mu haɗa hannu da NCC, NIMC, domin tabbatar da cewa mun baiwa ’yan Nijeriya tsarin zaɓe da fasaha mai inganci da kowa zai gamsu da shi.”

Farsesa Amupitan ya jaddada cewa za a duba harkokin sufuri da kayan zaɓe, inda ya yi nuni da cewa wasu motoci da ake amfani da su wajen kai kayan zaɓe sun tsufa kuma ba sa zuwa nesa sosai, sannan ba sa dawo da kayan bayan amfani da su.

Kan batun tsarin sakin sakamakon zaɓe ta intanet ta IReɓ, Amupitan ya ce kafin kotun ƙoli ta bayyana, ba a gaya wa ’yan Nijeriya cewa IReɓ ita ce kaɗai tsarin tattara sakamako ba.

“IReɓ ta kasance hanya ce kawai ta tabbatarwa da gwaji, amma dokokin da wannan majalisa ta tsara ba su kawar da tattara sakamakon hannu ba.”

Amupitan ya kuma jaddada buƙatar kafa hukumar bincike da hukunta laifukan zaɓe, domin inganta hukunci ga masu laifi a harkokin zaɓe, yayin da yake mai cewa a yanzu INEC ba ta da ƙarfin gudanar da bincike da hukunta waɗannan laifuka.

A madadin ‘yan majalisar Kogi, Sanata Sunday Karimi ya yaba da naɗin Amupitan, yana mai cewa, “Wannan ne karon farko Kogi ke da nata a matsayin Shugaban INEC. Mu bashi dama ya yi aiki domin tsarin zaɓenmu ya samar da sakamako mai kyau.”

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi fatan naɗin Amupitan zai inganta tsarin zaɓe, tabbatar da gaskiya, da ganin cewa duk ƙuri’u an ƙirga su yadda ya kamata.

Farfesa Amupitan ya ƙara da cewa, zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gyara duk wasu matsalolin da suka shafi kayan aikin 2023 da sauran harkokin zaɓe, domin samar da tsarin da zai gamsar da ’yan Nijeriya gaba ɗaya.

By ukarofi