Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirin fara sayar da kaso daga matatarsa ta tace mai domin ‘yan Nijeriya su samu damar mallakar wani ɓangare na abin da ya bayyana a matsayin “kadara ta ƙasa.”
Dangote ya sanar da hakan ne yayin taron Inaugural Annual Downstream Petroleum Week 2025 da kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin man fetur (Downstream) ya shirya a Abuja.
A cewarsa, wannan mataki na cikin shirin ba wa ‘yan ƙasa damar shiga cikin kasuwancin masana’antar, wanda zai ƙarfafa tattalin arziki da kuma mallakar albarkatu a cikin gida.
Babban jami’in tsare-tsare na Kamfanin Dangote Industries Limited, Aliyu Suleman, ya bayyana cewa shirin sayar da hannayen jarin zai bai wa ‘yan Nujeriya damar cin gajiyar nasarorin da matatar ke samu kai tsaye.
“A yau Nijeriya ta koma ƙasa mai fitar da man da aka tace, polypropylene da takin urea. Wannan babban cigaba ne a tarihinmu. Ba nan muke tsaya ba — za mu buɗe damar zuba jari domin ‘yan Nijeriya su mallaki wani kaso daga wannan kadara ta ƙasa,” inji Suleman.
Dangote ya kuma karyata zarge-zargen cewa yana neman mallakar kasuwar man fetur shi kaɗai, yana mai cewa babu wani takunkumi da ke hana wani ɗan kasuwa gina masana’antar tace mai a ƙasar.
“Masu kuɗi da dama sun fi son zuba jari a ƙasashen waje maimakon gina masana’antu a gida. Amma mu mun zaɓi hanya ta daban — gina a gida, ɗaukar ma’aikata a gida, da samar da kayayyaki a gida. Kada mu yi amfani da kalmar monopoly don hana ci gaba; babu wanda aka hana saka jari,” inji shi.
Dangote ya kuma jaddada cewa gwamnati na da rawar da za ta taka wajen ƙarfafa manufofin masana’antu da ke taimakawa ci gaban kasuwanci, ƙirƙira, da gasa a fannin man fetur.
Ya ce kusancin Nijeriya da albarkatun man fetur da iskar gas yana da babbar dama ta bunƙasa masana’antun tace mai da ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida.
