Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
A wani ɓangare na bikin ranar abinci ta duniya, ƙungiyar Mata Manoma ta Nijeriya NAWAIA reshen Jihar Zamfara, ta bai wa mata 114 tallafi don bunƙasa sana’ar noma da kuma magance ƙalubalen rashin isasshen abinci a jihar.
Da take jawabi yayin taron a Gusau jiya Alhamis, shugabar ƙungiyar, Hajiya Shemau Muhammad Nalado ta bayyana cewa, ƙungiyar ta baiwa mata 84 kayayyakin noma na zamani da ingantattun iri na zamani don samun nasarar sana’ar tasu ta noma.
Ta kuma sanar da cewa an bai wa mata marasa galihu 30 jari domin su bunƙasa ƙananan sana’o’in da suke yi kamar su ko dai, Awara, Waina da sauransu.
A cewarta, hanya mafi dacewa ta magance matsalar abinci ita ce inganta noma mai ɗorewa ta hanyar tallafa wa manoma da dabaru da fasahohi da kayan aiki na zamani don inganta amfanin gona da rage asara bayan girbi.
Ta ƙara da cewa, bayar da horo, da kuma bada lamuni, da sauran ababen more rayuwa ga mata manoma don inganta ayyukansu da gudummawar da suke bayarwa wajen samar da abinci ya zama dole don magance matsalar abinci a jihar.
Ta yaba wa uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda Lawal, bisa namijin ƙoƙarin da take yi wajen bunƙasa harkokin mata da bunƙasa noma a jihar.
Hajiya Shemau ta kuma yaba da irin tallafin da uwargidan gwamnan take bai wa ƙungiyar tasu a jihar.
Ta kuma jinjinawa Ma’aikatar Kasuwancin, Ma’adanai da Noma ta Jihar, Ofishin Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya, ofishin Hukumar Aikin Gona ACRESAL, NG-Cares, LIPAN, LPRESS, dangane da goyon bayan da suke baiwa ƙungiyar tasu a jihar don samun nasararta.
“A yau, muna bikin ranar abinci ta duniya wanda ke nuna muhimmancin samar da abinci, aikin noma mai ɗorewa da rage yunwa a duniya domin alƙaluma sun yi nuni da cewar kimanin kashi 9.2 na al’ummar duniya na fuskantar yunwa,” Hajiya Shemau ta ƙara da cewa.
A nata jawabin, uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa ƙungiyar bisa tallafin da take bai wa mata marasa galihu a jihar.
Ta kuma tabbatar wa ƙungiyar Mata Manoma ta Jihar cewar, gwamnatin jihar ta hannun ofishinta za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da kungiyar mata ta Nijeriya reshen jihar domin inganta bunƙasa samar da abinci a jihar.
