Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanda a Nijeriya (PSC) ta sake jaddada cewa ba ta da hurumin naɗawa ko tsige Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a kan ƙarewar wa’adinsa a ofis.
“Hukumar ba ta da hurumin da Kundin Tsarin Mulki ya ba ta na tantance naɗin ko ficewar Sufeto-Janar na ‘yan sanda,” inji mai magana da yawun PSC Ikechukwu Ani a wata sanarwa a ranar Litinin.
Bayanin hakan ya biyo bayan umarnin da hukumar ta PSC ta bayar a ranar Juma’a, inda ta umarci jami’an ‘yan sanda masu shekaru 60 ko kuma waɗanda suka yi aiki na tsawon shekaru 35 da su gaggauta yin ritaya. Matakin dai ya tayar da hankalin Egbetokun, wanda ya cika shekara 60 a bara.
Ani ya jaddada cewa umarnin ya shafi jami’an hukumar PSC ne kawai kuma bai shafi IGP ba, wanda shugaban ne kaɗai zai iya naɗin ba majalisar ‘yan sanda ba.
“Doka a bayyane take kan wannan batu,” inji Ani. “Sufeto-Janar na ‘yan sanda shugaban ƙasa ne ya naza shi, kuma tsige shi ya biyo bayan bin tsari kamar yadda tsarin mulki ya tsara.”
Ya bayyana cewa, Sufeto Janar ɗin naɗin shugaban ƙasa ne, wanda aka zaɓƙ bisa shawarar hukumar ‘yan sanda.
“Hukumar a taronta na musamman na farko na hukumar gudanarwa ta 6 a ranar Juma’a, 31 ga Janairu, 2025, ta yi nazari ne kawai kuma ta yanke shawara kan daidaita ranar naɗin farko na CADET ASPs/Inspector Force Entrant. Wannan ba shi da alaƙa da Sufeto-Janar na ‘yan sanda ko ofishinsa,” inji Ani.
Ya kuma ƙara jaddada cewa, “Hukumar na son bayyana cewa ta gamsu da girman ikon da Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya ba ta, kuma ba ta da sha’awar neman karin wasu madafun iko da doka ta ba ta.”
Ani ya ƙarƙare da cewa, hukumar ta PSC ta ci gaba da ƙulla alaƙa ta ƙud da ƙud da babban sufeton ‘yan sanda domin amfanin rundunar ‘yan sandan Nijeriya baki ɗaya.
Hukumar ta PSC ta jaddada aniyar ta na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shugabannin ‘yan sanda tare da kiyaye dokokin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada wajen sa ido kan sauran jami’an rundunar.
